Tarihin Sarkin Zazzau Jafaru Dan Isyaku 1935-1959
[ad_1]
Bayan sun taru ne Sarkin ya fara jawabi kamar haka “wasu daga cikinku waɗanda suke kusa sun ji mummunan labarin abinda yake faruwa a garin Zangon Kataf. Dan haka ina umurtar kowa daga cikin ku ya shirya ya kuma tabbatar da cewar gobe da safe kafin ƙarfe 9:00 na safe yana cikin mota. Duk wanda ya gaza bin wannan umurnin ya jira daga baya ya amshi kuɗin mota wurin Wali Umaru Hakimin Lere ya same mu a Zangon Kataf.
Kamar yadda Magajin Busa ya ce kowa ya bi wannan umurni na Mallam Jafaru, har da ma Jakadu duk sun kasance a mota kafin ƙarfe 9:00 na safe. Kimanin ƙarfe 9:00 daidai Sarkin Zazzau Mallam Jafaru ya fito daga masaukin shi da rawani mai haske akan shi, ya kuma rufe kan shi da ƙoƙuwar alkyabba. A hannunshi na hagu Kuma yana riƙe da Dala’ilu, hannun shi na dama kuma yana riƙe da farin charbi. Da fitowar shi bai ma kowa magana ba alama kawai ya yi da hannu na idan motarsa tayi gaba duk sauran ayarin motocin su bishi a baya.
- Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya
- Illolin Da Yawace-yawacen Mata Ke Haifarwa Ga Zamantakewar Aure
Mallam Jafaru ya bar Lere ya nufi Zangon Kataf kai tsaye. A wancan lokacin, lokacin rani ne hanyar data haɗa Lere da Zangon Kataf tana cikin mummunan yanayi. Saboda munin wancan hanyar tafiyar daga Lere zuwa Zangon Kataf yana ɗaukar Sarkin da tawagar shi tsawon tafiyar yini ɗaya sannan ya kai kusa da garin Zangon. Motar Sarkin da tawagar shi sun tsaya a Gonar Ganye, wacce take kusa da garin Zangon Kataf. Cikin hanzari Baraya Hamisu ya fito ya buɗe ma Sarkin ƙofa, Mallam Jafaru ya fito daga mota, suma yan tawagar Sarkin suka fito daga motocinsu amna banda tsoffafi da Jakadu.
Sarkin Zazzau Mallam Jafaru Dan Isyaku, ya fuskanci garin Zangon Kataf yayi ta addu’a kusan tsawon mintina arba’in sauran yan tawagar Sarki na amsawa da Amin. Bayan Sarkin na Zazzau ya kammala addu’oin na shi ya juyo wurin mutane ya amsa gaisuwa, sannan ya tabbatar musu da cewar da yaddar Allah babu abinda zai faru. Suka kintsa suka shiga garin Zangon Kataf. Mallam Jafaru Dan Isyaku ya umurci kowa ya koma bayan shi, shi ne zai shiga gaba ya shugabanci wannan tawagar a shiga Zango.
Shigowa garin Zango da Mallam Jafaru ya yi, ya yi mutuƙar girgiza kabilun garin. Sarkin Zazzau Mallam Jafaru da ya shigo garin yaga sun kewaye ko ina a garin. Izzarshi da kwarjinin shi ya yi mutuƙar yin tasiri a wurinsu. Waɗannan kabilu masu ƙoƙarin tada ƙayar baya, suna ganin Sarkin da tawagar shi suka tarwatse sukai cikin daji a guje. Nan take Sarkin ya umurci makaɗan Sarki da yan bindiga su fara aikinsu. Ƴan bindiga suka fara harbi a sama, makaɗa da mabusa suka shiga aikinsu.
Nan take Hausawan garin Zango suka shiga fitowa daga gidajensu, wasu daga mavoyarsu. Al’umma suka shiga murna da farin ciki suna ma Sarkin jinjina. Mai son ya samu cikkakken labarin nan sai ya duba littafi mai suna Mallam Jafaru Dan Isyaku The Great Emir Of Zazzau shafi 436-439 wanda Usman Dalhatu iliyasu ya rubuta.
[ad_2]
Source link