Arewa Maso Yamma: Hatsarin mota ya rutsa da wakilan APC na Katsina

[ad_1]



Hatsarin mota ya rutsa da wasu wakilan jam’iyyar APC daga Ƙaramar Hukumar Sabuwa a Jihar Katsina, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa taron jam’iyyar na shiyyar Arewa Maso Yamma.

Ɗaya daga cikin wakilan, Dalhat Machika, ya rasu a hatsarin.

Wasu da dama sun ji rauni, ciki har da tsohon Mataimakin Gwamnan jihar, Sirajo Umar Damari da shugaban jam’iyyar APC na Ƙaramar Hukumar Sabuwa.

A cewar wata sanarwa daga Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamna Dikko Umaru Radda, waɗanda suka ji rauni suna samun kulawa a Asibitin Yusuf Dantsoho Memorial da ke Tudun Wada a Jihar Kaduna.

Bayan kammala taron, Gwamna Radda ya ziyarci asibitin don duba halin da suke ciki.

Gwamnan ya kasance tare da manyan jami’an gwamnati, ciki har da Mai Bai Wa  Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Siyasa, Ibrahim Kabir Masari.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *