Mutum 5 ’yan gida ɗaya sun rasu a hatsarin mota a Yobe

[ad_1]



Aƙalla mutum biyar ’yan gida ɗaya ne suka rasu a wani hatsarin mota da ya auku a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri a Jihar Yobe.

Hatsarin ya faru ne a ranar Laraba, inda ya shafi mazauna Ƙaramar Hukumar Potiskum, lamarin da ya jefa al’umma cikin jimami.

Wani ɗan uwan mamatan, Dahiru Musa Talba, ya ce mutum biyar sun rasu, yayin da wasu uku suka jikkata.

An garzaya da waɗanda suka ji rauni zuwa Babban Asibitin Damaturu domin kula da su.

Talba, ya bayyana lamarin a matsayin mai matuƙar tayar da hankali, inda ya tabbatar da faruwar hatsarin a wani saƙo da ya wallafa a Facebook.

Kakakin rundunar ’yan sanda a Jihar Yobe, SP Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da faruwar hatsarin.

Ya ce mutum biyar sun rasu nan take, yayin da wasu suka jikkata, inda ya ce suna ci gaba da bincike domin gano musabbabin faruwar hatsarin.

Waɗanda suka rasu sun haɗa da Hajjagana Dahiru Zayi, Ibrahim Dahiru Zayi, Muhammad Dahiru Zayi, Hauwa Dahiru Zayi, da kuma wani ɗan uwansu.

Mazauna yankin sun bayyana lamarin a matsayin abin tausayi, tare da kira ga direbobi da su riƙa taka-tsantsan yayin tuƙi.

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bayyana alhininsa kan lamarin tare da miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan.

Ya kuma yi addu’ar Allah Ya gafarta musu, Ya kuma bai wa iyalan haƙurin jure wannan babban rashi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *