Kotu ta ba da umarnin kamo waɗanda ake zargin na alaƙa da Bello Turji




Wata Kotun Tarayya da ke Abuja, ta bayar da umarnin kamo wasu mutum biyar da ake zargin na alaƙa da ƙasurgumin ɗan bindigar nan da ake nema ruwa a jallo, Bello Turji.

Mai shari’a Emeka Nwite ne, ya bayar da umarnin a ranar Laraba bayan waɗanda ake tuhumar sun gaza halartar kotu domin fara shari’arsu.

Lauyan Gwamnatin Tarayya ya nemi kotu ta bayar da takardar izinin kama su saboda rashin halartar su kotu.

Mutanen sun haɗa da Musa Kamarawa, Abubakar Hashimu (wanda aka fi sani da Doctor), Samuel Chinedu da Lucky Chukwuma.

Lauyansu ya ce ya yi mamakin rashin zuwansu kotun, duk da cewa sun yi masa alƙawarin za su halarta.

Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da su ne a watan Disamban 2024.

Ana zarginsu da taimaka wa ƙungiyoyin ’yan ta’adda ta hanyar samar musu da ƙwayoyi, abinci, kakin sojoji da na ’yan sanda, da kayan gini zuwa sansanoninsu da ke jihohin Zamfara, Sakkwato da kuma Jihar Kaduna.

Kotun ta ɗage shari’ar zuwa ranar 24 ga watan Fabrairu domin ci gaba da sauraron ƙarar.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *