Ci Gaban Tattalin Arzikin Kasar Sin Ba Tare Da Tangarda Ba A 2025 Ya Karfafa Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

[ad_1]

A jiya, hukumar kididdiga ta kasar Sin ta gabatar da bayanan tattalin arzikin kasar Sin na shekarar 2025, matakin da ya baiwa duniya wata dama mai kyau ta fahimtar ci gaban Sin. Wannan ba takardar bayanan ci gaban tattalin arzikin kasar Sin ce kadai ba, har ma takarda ce dake karfafa gwiwar kasashe masu tasowa a halin da ake ciki, na rashin tabbas a fannin bunkasar tattalin arzikin duniya. Bayanan sun nuna cewa, a shekara ta 2025, a karon farko GDPn kasar Sin ya wuce Yuan tiriliyan 140, wanda ya karu da kashi 5% idan aka kwatanta da shekarar da ta gabaci hakan.

Karuwar da Sin ta samu ya zarta hasashen da IMF ta yi kan kasashe masu wadata, wato kashi 1.8% a 2025, ya kuma bayyana rawar da Sin ta taka a fannin ingiza bunkasar tattalin arzikin duniya baki daya. Kamar yadda darektan hukumar kididdiga ta Sin Kang Yi ya jaddada, “ginshikin ingantacciyar bunkasar tattalin arzikin Sin a dogon lokaci bai canja ba.” Ci gaban da Sin take samu na bayyana dorewa, da juriyarta a bangaren raya tattalin arziki, duk da yanayi maras tabbaci, da sarkakiya da ake fuskanta a duniya. Dalilin da ya haifar da hakan shi ne ingantattun ginshikan tattalin arzikinta.

Muna iya ganin hakan a cikin alkaluman da aka fitar, wato tushenta mai inganci, da yin kwaskwarima a gida, bisa dogaro da bunkasar sabbin karfin samar da kayayyaki da hidima mai dorewa.

A shekara ta 2025, adadin darajar masana’antar manyan fasahohi a duk fadin kasar Sin ya karu da kashi 9.4%, wanda ya fi bunkasar masana’antu gaba daya sauri. Yawan kayayyakin “sabbin nau’ika uku”, wato motocin lantarki, da batirin lithium, da allunan samar da wutar lantarki ta hasken rana ya karu sosai, inda karuwar motocin lantarki da aka samar ya kai kashi 25.1 %, wadanda suka zama sabon injin dake ingiza bunkasuwar masana’antu. Wannan ba sauye-sauyen masana’antu ne kadai ba, har ma sauye-sauye ne na ci gaba—ci gaban tattalin arziki yana canzawa daga dogaro da tsoffin abubuwa zuwa bunkasa ta hanyar fasaha da kimiyya.

Canjin tsarin tattalin arzikin Sin, musamman bunkasar “sabon karfin samar da kayayyaki da hidimomi masu karko,” ya samar da damammaki ga nahiyar Afirka, wadda ke kokarin samun ci gaban masana’antu da zamanintar da al’umma, kana ma’anar hakan ta zarce batun zuba jari da ciniki kadai, inda ta kai ga samfurin hadin gwiwa, da ci gaban kasashe masu tasowa. Cikakken tsarin hada na’urorin samar da wutar lantarki masu amfani da iska, da hasken rana ta Sin, ya ba da damar yin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen nahiyar Afirka, don inganta masana’antu ba tare da gurbata muhalli ba a Afirka.

Alal misali, tashoshin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana, da iska da kamfanonin Sin suka gina a Afirka ta Kudu, da Morocco a shekara ta 2025, ba wai kawai sun samar da wutar lantarki mai tsabta ba ce, har ma hakan ya samar da zarafi na hada kayan aiki da horar da ma’aikata da sauransu waje guda, tare da haifar da sabon tsarin masana’antu mai kiyaye muhalli, da dimbin guraben aikin yi.

A shekara ta 2025, duk da rashin karfin raya tattalin arzikin duniya, da bullowar manufar kariyar cinikayya da sauyin yanayi, tattalin arzikin Sin ya nuna halaye na ” ci gaba, da kokarin kirkire-kirkire, da wani yanayi mai karko.” Ainihin karko, ya fito ne daga yin kwaskwarima a gida, da bude kofa ga waje da rungumar sabbin fasahohi. Ta hanyar bunkasa “sabon karfin samar da kayayyaki da hidimomi masu karko,” Sin ta samar da sabon yanayi na tabbas ga kanta da kuma abokan hadin gwiwarta. Ga Afirka, wannan tabbaci yana bayyana cewa, Sin wata abokiyar hadin gwiwa ce mafi kyau.

A sabuwar shekarar nan, duk da cewa tattalin arzikin Sin zai ci gaba da fuskantar kalubaloli daban-daban, ba shakka kasar za ta iya ci gaba da samarwa kasashe masu tasowa, ciki har da kasashen Afirka, da karin damammaki da yanayi na tabbas. (Mai rubuta: MINA)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *