An fitar da sunayen mutum 177 da aka sace a harin coci a Kaduna

[ad_1]



Al’ummar ƙauyen Kurmin Wali da ke Jihar Kaduna, sun fitar da sunan mutum 177 da aka sace bayan harin da wasu ’yan bindiga suka kai musu.

Rahotanni sun ce harin ya faru ne a ranar Lahadi, lokacin da mutane ke ibada a wasu coci daban-daban a yankin.

Maharan sun shiga cocin, tare da suka tattara masu ibada, sannan suka kora su zuwa cikin daji.

Daga baya, al’ummar ƙauyen sun ce mutane 10 sun samu nasarar tserewa daga hannun ’yan bindigar.

A ranar Talata, rundunar ’yan sandan Najeriya, ta tabbatar da faruwar lamarin, bayan da ta musanta shi da farko.

A wata sanarwa da kakakin rundunar, Benjamin Hundeyin, ya fitar, ya ce binciken da sashen tattara bayanan sirri na rundunar ya nuna cewa an yi garkuwa da mutanen.

Al’ummar ƙauyen sun ce sun tattara sunayen mutanen da aka sace ne daga coci-cocin da aka kai hari, tare da haɗa shekarun mutanen da abin ya shafa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *