Yawan Hatsin Da Kasar Sin Ta Noma Ya Kai Wani Sabon Matsayi Na Koli A 2025

[ad_1]

Kasar Sin ta sake samun wani gagarumin girbin hatsi mai albarka a bara, wanda ya kara yawan amfanin gonar da aka samar duk da matsalolin fari, ambaliyar ruwa da kuma zarcewar ruwan sama a wasu sassan kasar, kamar yadda bayanai daga ma’aikatar kula da harkokin noma da karkara suka bayyana a yau Alhamis.

A cewar ma’aikatar, yawan hatsin da aka noma ya kai kimanin tan miliyan 714.9 a shekarar 2025, wanda ya karu da tan miliyan 8.4 idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata, kana yawan amfanin gonar ya ci gaba da kasancewa sama da tan miliyan 700 a tsawon shekaru biyu a jere.

An samar da sabbin gonaki masu inganci tare da daga darajarsu da suka kai fadin ma’aunin mu miliyan 75.68, watau kwatankwacin hekta miliyan 5.05, sannan an samar da wasu makamantansu da suka kai fadin ma’aunin mu biliyan daya, watau kwatankwacin hekta miliyan 66.67.

Kazalika, gudummawar da kimiyya da fasaha ke bayarwa ga bunkasa harkar noma ta haura kaso 64 cikin dari. Haka nan, cikakken tsarin amfani da injina na zamani wajen noma, shuka, girbi da adanawa ya kai kaso 76.7 cikin dari, yayin da adadin na’urori masu tashi sama da ake amfani da su a bangaren aikin gona ya wuce 30,000, kana fadin yankin da ake aikin gonar ya haura fadin ma’aunin mu miliyan 460, watau kimanin hekta miliyan 30.67 a bisa mizanin shekara-shekara. (Mai Fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *