Yadda maganin sauro ya yi ajalin magidanci da iyalinsa a Kano
[ad_1]
Wani magidanci tare da ɗaukacin iyalinsa huɗu sun rasu sakamakon wata gobara da ta tashi a sanadin kunna maganin sauro a layin Baba Impossible da ke Unguwar Kundila, da ke Ƙaramar Hukumar Tarauni a Jihar Kano.
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta tabbatar da tashin wutar da misalin ƙarfe 4:13 na Asubar ranar Laraba.
Mai magana da yawun hukumar, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya ce sun samu kiran wani ma’aikacinsu, HFS Abba Datti, game da gobarar.
A cewarsa ba tare da ɓata lokaci ba suka tura jami’ansu daga hedikwatar hukumar zuwa wajen da gobarar ta tashi.
“Lokacin da muka isa, mun ga wani gida mai girman ƙafa 40 da 30 yana ƙone gaba ɗaya. Gobarar ta shafi ɗakuna biyu, falo, bayan gida, da kuma ɗakin girki,” in ji sanarwar.
Mutane biyar ne gobarar ta rutsa da su; mai gidan mai suna Shodandi mai shekara 43, matarsa Rafi’a mai shekara 30.
Ragowar kuma ’ya’yansu ne; Mardiya Shodandi mai shekara uku, Yusira Shodandi ’yar shekara ɗaya da rabi da Aminu Shodandi ɗan watanni 12.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Huɗu daga cikinsu; uba, uwa, da ƙananan yara biyu sun ƙone kafin a ceto su. Amma an samu damar ceto Aminu ɗan watanni 12.”
Hukumar ta miƙa saƙon ta’aziyyarta ga iyalan mamatan, ta kuma ta gargaɗi mutane da suke kula sosai, musamman a lokacin sanyi.
Bincike ya nuna cewa gobarar ta samo asali ne daga maganin sauro da matatan suka kunna a falo, sannan suka yi barci.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link