Matatar Dangote ta ci gaba da sayar da man fetur a naira
[ad_1]
Matatar Dangote ta janye ƙudirin dakatar da sayar da man fetur a naira, tana mai cewa abokan hulɗarta za su iya sayen man ta hanyar amfani da naira maimakon dala.
Lamarin na zuwa ne ƙasa da kimanin sa’o’i 24 bayan matatar ta sanar da dakatar da cinikayyar man fetur da naira.
Bayanai sun an samu wannan sauyi ne bayan Shugaban Hukumar Tattara Haraji na Najeriya (FIRS), kuma shugaban kwamitin amfani da naira a kasuwancin man fetur, Dokta Zacch Adedeji ya shiga tsakani.
Gwamnatin Najeriya ce ta hannun kamfanin man fetur na ƙasar wato NNPCL ta kafa kwamitin domin ganin ana sayar da man fetur ga dilolin cikin Najeriya a naira maimakon dala.
Tun a ranar Juma’ar ce Matatar Dangote ta sanar da dakatar da amfani da naira wajen sayar da fetur, lamarin da ta ce zai fara aiki a ranar Asabar, 28 ga watan Satumba saboda a cewarta nauyin ya mata yawa, kuma ba za ta iya ci gaba ba.
Sai dai kuma a yammacin jiya Asabar ɗin matatar ta sake fitar da wata sanarwa, inda ta ce za ta ci gaba da sayar da fetur ɗin a naira.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link