Yadda ƙarfen gidan tsohon kwamandan Hisbah na Ganduje da raunata yara 5 a Kano
[ad_1]
Mazauna unguwar Sharaɗa Rinji da ke cikin birnin Kano sun yi kira da a ɗauki mataki kan wasu ƙarafa masu kaifi da ke jikin relar gidan Muhammad Harun Ibn Sina, tsohon Babban Kwamandan Hisbah ta Jihar Kano, wanda ya jikkata yara da dama, har ma ya yanke yatsun biyu daga cikinsu.
Ibn Sina shi ne kwamandan Hisbah a lokacin mulkin tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje.
Ɗaya daga cikin waɗanda abin ya rutsa da ’ya’yansu, Jamilu Ahmad Bala, ya ce ’yarsa ta rasa yatsanta bayan hannunta ya makale a cikin ƙarafan yayin da take wasa a lokacin da aka fita shan iska a makaranta.
Jamilu ya shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru makonni biyu da suka gabata.
“Nan take ƙarfen ya yanke mata yatsa lokacin da ya makale. Daga baya muka gano cewa ƙarafan sun taɓa ji wa hatta ɗan maigidan rauni, hakan ya sa ya gyara waɗanda ke cikin gidansa, amma ya bar waɗanda masu kaifi ne kuma masu hatsari,” in ji Jamilu.
Ya ƙara da cewa aƙalla jimillar yara biyar sun ji munanan raunuka da ƙarafan, ciki har da wata yarinya da ita ma yatsanta ya yanke.
Bala ya ce an kai rahoton lamarin ga Mai Unguwar yankin, inda Ibn Sina ya nemi afuwa kuma ya yi alkawarin ziyartar ‘yar tasa a asibiti.
Wani mazaunin unguwar, Hayatu Lawal Abdullahi, ya ce ƙarafan ba wai kawai suna barazana ga lafiyar yara ba ne, har ma sun shigo kan hanya.
“Idan Ma’aikatar Ƙasa ko hukumar tsara birane ta KNUPDA suka duba wurin ma, za su iya tuhumar shi da cin hanya. Akwai hanyoyin ƙawata gaban gida masu kyau na hanyar amfani da furanni ba ƙarfe mai kaifi ba. Muna son a cire ƙarafan gaba ɗaya don kauce wa ƙarin jikkata wasu yaran,” in ji Abdullahi.
Yara a unguwar ma sun bayyana irin illar da ƙarafan suka yi musu. Aisha Danjuma mai shekara 12, ta ce ita ma ƙarfen ya yanke mata yatsa bara kuma har yanzu na yi mata ciwo.
Shi ma wani yaro mai suna Aliyu Aliyu Hamza, ya ce ya ji rauni a goshinsa yayin da yake ƙoƙarin ciro ƙwallon shi da ta faɗa cikin ƙarafan.
Da aka tuntube shi, Ibn Sina ya yi watsi da ƙorafe-ƙorafen da cewa “kawai ƙoƙari ake yi a ɓata masa suna a kafafen yaɗa labarai,” yana mai jaddada cewa ya riga ya gyara ƙarafan tun tuni.
“Allah ne ya ƙaddara hakan. Tun da suka yi ƙorafi na sayi ƙarafa na sa aka rufe ramukan masu kaifi kuma aka turo min bidiyon aikin na gani saboda ba na gari. Kuma na gamsu cewa an gyara wurin mai matsala, sai kawai na sake jin su a kafafen yaɗa labarai. Wannan yunƙuri ne kawai na ɓata min suna,” in ji shi.
Daga nan ne ya tura wakilinmu zuwa wajen Mai Unguwar yankin, wanda ya ƙi yarda ya ce komai a kan batun, yana mai cewa ana ƙoƙarin warware lamarin a cikin gida.
Amma duk da haka, mazauna unguwar sun tsaya kai da fata cewa dole ne a cire ƙarafan gaba ɗaya, suna masu cewa gyaran da aka yi bai wadatar ba wajen tabbatar da kare faruwar hatsarin a nan gaba.
Sharaɗa Rinji dai na cikin unguwannin masu ƙanana da matsakaitan ƙarfi a cikin birnin Kano, inda dubban jama’a ke rayuwa a ciki.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link