2027: Jam’iyyar Labour Ta Ware Tikitin Takarar Shugaban Ƙasa Ga Kudancin Nijeriya


Shugabar jam’iyyar Labour ta kasa, Nenadi Usman, ta bayyana cewa jam’iyyar ta ware tikitin takarar shugaban kasa na shekarar 2027 ga yankin Kudancin Nijeriya.

Usman ta bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja, inda ta ce tuni an kammala yanke wannan shawara a cikin jam’iyyar.

“Mun dauki wata tabbatacciyar shawara guda, wato ba za mu tsayar da dan takara daga Arewacin Nijeriya ba. Mun ware wannan kujera ga Kudancin Nijeriya.

“Don haka idan wani dan Arewa ya zo yanzu yana son tsayawa takara, tabbas ba za mu amince da hakan ba,” in ji ta.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *