Kasar Sin Ta Cimma Burinta Na Shekarar 2025 Da Mai Da Hankali Kan Kirkire-kirkire Da Bukatun Cikin Gida
[ad_1]
Kasar Sin ta cimma manyan burikanta na ci gaban tattalin arziki da zamantakewa na shekarar 2025, tare da samun bunkasa ba tare da tangarda ba, da karfafa juriya da kuma manufofi da ke samar da manyan fa’idodi ga iyalai, kamar yadda babban jami’in tsare-tsaren tattalin arzikin kasar ya bayyana a yau Talata.
Wang Changlin, mataimakin shugaban hukumar tsara ci gaban kasa da gyare-gyare (NDRC), ya shaida wa taron manema labarai na majalisar gwamnatin kasa cewa hukumomin kasar Sin za su gudanar da bincike tare da gabatar da wani shiri na aiki daga shekarar 2026 zuwa 2030 domin fadada bukatar cikin gida.
Ya ce kasar Sin za ta kuma kara tallafa wa sabbin kirkire-kirkire ta hanyar daukar matakai kamar amfani da asusun ba da jagoranci kan jarin kamfanoni na kasa, da kuma inganta tura kudaden saka hannun jari na gwamnati.
Da yake tsokaci kan hangen gaba, jami’in na NDRC Zhou Chen ya ce tsarin tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da inganta a shekarar 2026, inda ginshikan samar da ci gaba ke kara karkata zuwa ga sashen kirkire-kirkire. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link