Kwankwaso Bai Je Ƙasar Waje Neman Magani Ba – Kwankwasiyya
Ƙungiyar Kwankwasiyya ta musanta rahotannin da ke cewa jagoranta kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, an kai shi ƙasashen waje neman magani.
A wata sanarwa, ƙungiyar ta bayyana cewa Kwankwaso ya yi tafiya ne saboda wani lamari na ƙashin kansa, ba don neman magani ba.
- GDPn Nijeriya Ya Yi Ƙasa Fiye da Na Shekaru 20 da Suka Wuce A Zamanin Obasanjo — Hashim
- HOTUNA: Ɗan Ganduje Ya Ziyarci Kwankwaso A Kano
Kakakin ƙungiyar, Mansur Kurugu, ya ce tafiyar Kwankwaso ba ta da alaƙa da rashin lafiya ko neman magani.
Wasu fitattun ’yan siyasa a Jihar Kano sun wallafa saƙonni a shafukan sada zumunta suna cewa wai an kai Kwankwaso waje neman magani saboda rashin lafiya da yake fama da ita.
Sai dai wani magoyin bayan Kwankwaso, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce waɗannan rahotanni aikin maƙiyansa ne.
Ya ƙara da cewa a satin nan Kwankwaso ya ziyarci Kasuwar Singer domin jajanta wa ’yan kasuwar da gobara ta shafa, inda dubban mutane suka tarbe shi.
Ya ce wannan na nuni a fili cewa Kwankwaso yana cikin ƙoshin lafiya kuma yana ci gaba da ayyukansa yadda ya kamata.