Ramadan: NUJ ta tallafa wa iyalan ma’aikatan da suka rasu da kayan abinci a Jigawa

[ad_1]



Ƙungiyar ’yan jarida ta ƙasa (NUJ) reshen Jihar Jigawa, ta raba kayan abinci da kuɗi ga iyalan ma’aikatan da suka rasu da waɗanda suka yi ritaya a jihar.

An gudanar da rabon tallafin a hedikwatar ƙungiyar da ke Dutse, inda aka ba su buhunan shinkafa mai nauyin kilo 25, taliya, da kuma kuɗi Naira 320.

Babban Manajan FRCN Horizon FM, Alhaji Habibu Nuhu Kila, ya yaba da wannan shiri, yana cewa yana nuna kulawa da jin daɗin ’yan jarida.

Ya ce dattawan ƙungiyar za su ci gaba da mara wa irin wannan shiri baya.

Shi ma Manajan Freedom Radio Dutse, Alhaji Ali Falaki, ya ce shirin abin yabawa ne domin yana taimaka wa iyalan mamatan, tare da alƙawarin ci gaba da tallafa wa ƙungiyar.

Shugaban NUJ na jihar, Kwamared Isma’ila Ibrahim Dutse, ya ce ƙungiyar za ta ci gaba da kula da iyalan mamata da waɗanda suka yi ritaya.

Ya kuma ce shirin ya samu goyon bayan gwamnatin jihar ƙarƙashin gwamna Umar Namadi.

Da yake magana a madadin waɗanda suka amfana, Alhaji Salmanu Adamu Rishi, ya gode wa NUJ bisa wannan taimako a watan Ramadan, tare da yi wa mambobin ƙungiyar fatan alheri.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *