China ta yi martani kan barazanar Trump ta kai hari Najeriya

[ad_1]



Ƙasar China ta soki abin da ta kira yunƙurin Shugaban Amurka Donald Trump na yin katsalandan cikin harkokin cikin gida na Najeriya, inda ta bayyana cikakken goyon bayanta ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar, Mao Ning, ce ta bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Talata, a matsayin martani kan barazanar Shugaba Trump ta tura sojojin Amurka zuwa Najeriya domin yaƙi da abin da ya kira kisan kiyashi ga Kiristoci.

Trump, wanda ya yi ikirarin cewa ana kisan Kiristoci a Najeriya, ya zargi gwamnatin Shugaba Tinubu da yin biris da zarge-zargen, yana mai cewa Amurka za ta iya ɗaukar mataki, ciki har da kai hare-hare ta sama ko ta ƙasa.

Sai dai gwamnatin Najeriya ta musanta zargin, tana mai cewa irin wannan kalami ba ya nuna haƙiƙanin halin da ake ciki a ƙasar.

A martaninta, Mao Ning ta ce, “China tana da kyakkyawar alaƙa da Najeriya, kuma muna bai wa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu cikakken goyon baya wajen gudanar da mulki bisa tsarin da ya dace da yanayin ƙasarsu.”

A cewarta, China ba ta goyon bayan ƙasashen da ke amfani da addini ko batun haƙƙin ɗan Adam a matsayin hujjar yin katsalandan cikin harkokin wasu ƙasashe masu cikakken ‘yanci.

“Ina mai jaddada cewa China tana adawa da duk wani yunƙuri na barazana, takunkumi ko amfani da ƙarfin soja wajen tsoma baki cikin harkokin cikin gida na wata ƙasa,” in ji Mao Ning.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *