Hatsarin tankar Gas: Gwamna Inuwa Ya tallafa wa iyalai da N5m

[ad_1]



An gudanar da jana’izar mutane biyar da suka rasu a wani hatsarin tankar iskar gas a Karamar Hukumar Akko da ke Jihar Gombe.

Gwamnan Muhammadu Inuwa Yahaya, ya halarci jana’izar, inda bayyana bakin cikinsa kan mummunan hatsarin da ya faru a ƙauyen Lawanti, inda motar ta murƙushe mutane biyar tare da jikkata wasu.

Wadanda suka rasu sun haɗa da Babayo Bello Konkeje (60), Ahmadu Adamu Konkeje (43), Yahaya M. Manu Konkeje (40), Haruna Abdu Shulto (45) da Yana Alhaji Jarami Dunumari (51).

Gwamna Inuwa Yahaya, wanda ya halarci Sallar Jana’iza tare da iyalai da al’ummar yankin a Fadar Hakimin Lawanti, ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi ga iyalan mamatan kadai ba, da kuma ɗaukacin al’ummar Jihar Gombe.

Ya miƙa sakon ta’aziyya a madadinsa da gwamnatin jihar da mutanen Gombe baki daya.

“Mun zo ne domin juyayin al’ummar Lawanti bisa rasuwar waɗannan bayin Allah biyar. Muna roƙpn Allah Ya gafarta musu kurakuransu Ya kuma sa su cikin Aljannatul Firdaus,” in ji shi.

Gwamnan ya kuma yi ta’aziyya ga iyalan wasu mutane bakwai da suka rasu a wani lamari daban a yayin da suke tafiya Maiduguri a watan Disamba 2025, yana mai cewa al’ummar yankin sun fuskanci manyan rashe-rashe a cikin ƙanƙanin lokaci.

Ya yaba wa al’ummar Lawanti kan jajircewarsu da nutsuwa da suka nuna bayan faruwar lamarin ba tare da ɗaukar doka a hannunsu ba, yana mai cewa hakan ya nuna biyayya ga doka da kishin zaman lafiya.

Gwamna Yahaya ya tabbatar da cewa gwamnati za ta ɗauki matakan da suka dace domin kare faruwar irin haka a gaba, tare da bayyana bayar da tallafin naira miliyan biyar ga iyalan waɗanda suka rasu domin rage musu raɗaɗin rashin.

A nasa bangaren, Hakimin Lawanti, Alhaji Bello Hassan, ya gode wa gwamnan bisa halartar sallar jana’izar da nuna tausayawa da taimakon da ya bayar, yana mai bayyana hakan a matsayin jagoranci mai tausayi da kula da al’umma.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *