Za Mu Yi Duk Mai Yiwuwa Don Hana Iran Mallakar Makamin Nukiliya – Netanyahu
[ad_1]
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce bai kamata a bar Iran ta mallaki makamin nukiliya ba.
Ya faɗi hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar bayan harin haɗin gwiwar Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran, inda ya gode wa Amurka bisa goyon bayan da ta bayar.
- Ramadan: Lokutan Buda-Baki Da Sahur Na Azumi Na 11
- Shugaban Seychelles Ya Jinjina Wa Kasar Sin Game Da Nasarorin Da Ta Cimma
Netanyahu ya ce tsawon kusan shekaru 47 gwamnatin Ayatollah tana yin kalaman barazana ga Isra’ila da Amurka.
Ya kuma zargi cewa gwamnatin Iran ta jawo mutuwar Isra’ilawa da Amurkawa da dama, yana mai cewa saboda haka bai dace a bar ta mallaki makamin nukiliya ba.
A cewarsa, harin da aka kai zai iya bai wa mutanen Iran damar su sauya gwamnatinsu da kansu.
[ad_2]
Source link