GDPn Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 5.0% A Shekarar 2025

[ad_1]

Yau Asabar da safe, hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar da “Rahoton kididdigar tattalin arziki da zamantakewar al’umma na Jamhuriyar Jama’ar Sin na shekara ta 2025”.

Bisa kididdigar ta matakin farko, alkaluman hada-hadar tattalin arziki, watau GDP na kasar Sin a shekara ta 2025 sun kai Yuan tiriliyan 140.1879, wadanda suka karu da kashi 5.0% idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabace ta. Daga cikinsu, karuwar darajar masana’antun ayyukan gona ta kai Yuan tiriliyan 9.3347, wadda ta karu da kashi 3.9% idan aka kwatanta da shekarar 2024, kuma karuwar darajar masana’antun ayyukan samar da kayayyaki ta kai Yuan tiriliyan 49.9653, wadda ta karu da kashi 4.5%, kazalika karuwar darajar masana’antun ayyukan samar da hidimomi ta kai Yuan tiriliyan 80.8879, wadda ta karu da kashi 5.4%.

Daga cikinsu, bangaren kashe kudi ya taka rawar gani wajen karuwar GDPn kasar da kashi 2.6 cikin 100, kuma fitar da kayayyaki da hidima zuwa ketare ya jawo karuwar GDPn da kashi 1.6 cikin 100. (Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *