Ƴan Bindiga Sun Sake Garkuwa Da Wani Manomi A Kwara
[ad_1]
Jama’a a yankin Eruku da ke ƙaramar hukumar Ekiti a Jihar Kwara sun shiga ruɗani bayan wasu ƴan bindiga huɗu sun sake kai farmaki a ranar Lahadi, inda suka yi garkuwa da wani manomi mai suna Aasaru. Wannan harin na zuwa ne ƙasa da mako guda bayan gwamnatin tarayya ta kuɓutar da wasu masu ibada 38 na cocin CAC da aka sace a garin.
Shaidu daga yankin sun bayyana cewa maharan sun kai wa manomin hari ne a gonarsa da ke kan hanyar Koro, inda suka tafi da shi. Wannan ya dawo da fargabar da al’ummar yankin ke ciki saboda yawaitar hare-haren da suka addabi yankin a cikin wata guda.
Kakakin rundunar ƴansandan Jihar Kwara, Toun Ejire-Adeyemi, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce an samu rahoton sace manomin ne da misalin ƙarfe biyu na rana. Ta bayyana cewa jami’an ƴansanda da dakarun sa kai sun shiga aiki cikin gaggawa domin gudanar da bincike da kuma ceto wanda aka yi garkuwa da shi.
Ta ƙara da cewa rundunar ƴansandan Jihar Kwara ta ƙara tsaurara matakan tsaro a yankin, tare da tabbatar wa al’umma cewa suna aiki tukuru domin ganin an kuɓutar da manomin cikin koshin lafiya. Ta yi kira ga jama’a da su riƙa ba jami’an tsaro sahihan bayanai domin taimakawa wajen magance faruwar irin waɗannan hare-hare a nan gaba.
[ad_2]
Source link