Asarar Naira Biliyan 10.16 A Noman Bara: Manoma A Kaduna Sun Buƙaci Ɗaukin Gaggawa

[ad_1]

Manoma kimanin 2,143 a Jihar Kaduna, sun yi kira ga gwamnatin tarayya, da ta gaggauta kawo musu ɗauki, musamman ta fuskar ba su kayan aikin noma kyauta, ko kuma sayar musu da kayan a kan farashi mai sauƙi.

Sun yi wannan kira ne, biyo bayan mummunar asarar da suka tafka a kakar noman bara, wadda ta kai ta kimanin sama da naira biliyan 10.

  • Asusun NADF Ya Tallafa Wa Manoman Albasa 2,000 A Wasu Jihohin Kasar Nan
  • Ƙungiyar Manoma Na Neman Gwamnati Ta Tallafa Mata Da Kayan Aikin Noman Rani

Kiran nasu dai, na ƙunshe ne cikin wata takardar wasiƙa da suka rubuta tare da aikewa zuwa ofishin sakataren gwanatin tarayya da babban ministan ma’aikatar aikin noma da samar da wadataccen abinci da gwamnan babban bankin Nijeriya da  kuma sanatoci uku da ke wakiltar Jihar Kaduna.

Haka zalika, manoman waɗanda suka kasance sun fito ne daga shiyoyi uku na Kaduna, sun kuma koka a kan  faɗuwar da farashin Masara ya yi ɓagatatan, a dukkanin ɗaukacin faɗin wannan kasa, tare da kuma samun ƙarin farashin kayayyakin noma.

Manoman, sun rubuta wasiƙar ce ta hannun lauyansu, Barista Ehizogie Fidelis Imadojemu, wadda ke nuna cewa; manoman na gudanar da nomansu ne a ƙarƙashin shirin noman Masara, wanda Alhaji Rufai Muazu Dikko, da aka fi sani da Sarkin Labar, ke sanya ido.

Har ila yau, manoman sun ce; bisa wannan asarar da suka tabka, hakan ya sanya sun gaza mayar da kuɗaɗen da suka kashe, bayan sun yi girbi a kakar noman ta bara.

Suka ƙara da cewa, an faro shirin aikin noman ne, tun a shekarar 2017, wanda aka fara da kadadar noma kimanin  1,000, daga baya kuma aka faɗaɗa shirin zuwa kadada 10,000, inda aka noma kadada dubu 2,143 a Ƙananan Hukumomin Igabi, Soba, Kauru, Zariya da kuma Sabon Gari.

A cewarsu, a ƙarƙashin yarjejeniyar da aka ƙulla, Sarkin Labar ne ya samar da kuɗi da kuma kayan aiki, wanda kuma manoman idan sun yi girbi za su biya da Masara su kuma sayar da sauran abin da suka samu.

Haka zalika, sun bayyana cewa; buhun taki na NPK mai nauyin kilo 50, ana sayar da shi ne a kan kimanin naira 60,000, inda kuma na Urea, farashinsa ya ƙaru zuwa naira 50,000.

Sun ƙara da cewa, wannan dalili ne yasa jimillar kuɗin da suka kashe wajen noman kadada ɗaya ta Masara, kuɗin ya ƙaru zuwa sama da naira miliyan biyu daga naira miiyan ɗaya a bara.

Manoman sun yi gargaɗin cewa, idan har mahukuntan wannan ƙasa, ba su kawo musu ɗaukin gaggawa ba, ko shakka babu; manoma da dama a Nijeriya, musamman a yankunan Arewa, ba za su iya yin noma a kakar noma ta bana ba.

Kazalika, sun buƙaci babban bankin Nijeriya (CBN), ya samar musu da ɗauki na rage farashin kayan aikin noma da takin zamani, samfurin urea da za su yi amfani da shi a kakar noman ta bana.

A cewarsu, idan babban bankin Nijeriya ya kawo musu ɗauki, su kuma za su biya bankin da wani kaso na Masarar da suka noma, wadda za ta yi daidai da ɗaukin da bankin ya ba su, bayan sun girbe amfanin nasu a kakar ta bana.

Manoman sun kuma bayyana cewa, samar musu da ɗaukin; zai taimaka musu matuƙa wajen sayen amfanin gona a cikin farashi mai rahusa da ƙara samar da wadataccen abinci a ƙasar da kuma ƙara bunƙasa tattalin arziƙin ƙasar, musamman duba da cewa; zaɓukan 2027 na ƙara ƙaratowa nan da ɗan ƙanƙanin lokaci.

Don haka, a cewar tasu; hakan ne kawai zai ba su damar komawa gonakinsu a kakar ta bana, domin ci gaba da noma gonakin nasu.

Kazalika, sun kuma buƙaci son tattaunawa da jami’an gwamnati, domin samun damar tunkarar noman na kakar ta bana.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *