Shirin Shugaba Tinubu Na ‘Renewed Hope’ Zai Karfafa Wa Manoma Gwiwa – Oyebanji

[ad_1]


Gwamnan Jihar Ekiti, Mista Biodun Oyebanji, ya yaba wa shirin aikin noma na Shugaban Kasa Bola Tinubu (Renewed Hope), wanda ya ce; shirin zai kara wa mutane da dama kwarin gwiwar rungumar aikin manoma.

Kazalika, Oyebanji ya yaba da shirin, musamman duba da cewa; ana gudanar da shi ne ta hanyar yin amfani da fasahar zamani ta noma, wanda ya yi nuni da cewa; hakan zai jawo ra’ayin matasan jihar su rungumi aikin noma, inda hakan zai ba su damar bayar da tasu gudunmwar, wajen samar da wadataccen abinci a jihar ta Ekiti.

Ya bayyana hakan ne, a yayin kaddamar da farfado da wani katafaren gidan gona da ke yankin Eporo Ekiti, a Karamar Hukumar Emure da ke jihar.

Har ila yau, an kaddamar da gidan gonar ne daga cikin shirye-shiyen gudanar da bikin cikar gwamnan shekara uku a wa’adin shugabancinsa.

Kazalika, gwamnan ya kuma kaddamar farfado da wasu gidajen gona uku da ke yankunan Iyemero da kuma Ikere Ekiti, bisa nufin kara samar da wadataccen abinci a jihar, musamman domin rage farashin kayan abinci a jihar.

Gidajen gidan gonar uku, na daga cikin ayyukan shirin aikin gona da aka farfado da su, domin bai wa matasan da ke da sha’awar shiga aikin noma tare da kuma yin kiwon Kifi.

Gwamnan, wanda mataimakiyarsa, Madam Monisade Afuye ta wakilce shi a wajen taron ya sanar da cewa, baya ga sake farfado da gidajen gonar, wadanda firimiyan tsohuwar gwamnatin yamma, Cif Obafemi Awolowo ya samar da su, an kuma samar da wasu guda 13, domin bai wa matasan da ke yankin kwarin guiwar shiga aikin noma.

Kazalika, gwamnan ya bayyana cewa; an kuma samar da kayan aiki na zamani, wadanda za su bai wa matasan damar yin noma har zuwa karshen shekara, musamman domin inganta rayuwarsu da samar wa da kawunansu kudaden shiga da kuma yadda za su taimaka wa iyayaensu.

“Wadannan gidajen gona da muka kaddamar da su yau a yankunan Eporo, Emure da Iyemero, an sake farfado da su ne, domin a bai wa manoma kwarin gwiwar yadda za su rungumi aikin noma, domin su zama masu dogaro da kansu,“ in ji gwamnan.

“Kimanin matasa 5,000 zuwa yanzu aka dauka a karkashin wannnan shiri, musamman duba da cewa; matasan sun nuna cewa; a shirye suke su shiga aikin noma,” a cewar tasa.

“Muna kuma sane da marasa kishin da ke yunkurin yi wa wannan shiri zagon kasa, domin su ga cewa, aikin bai samu cin nasara ba, amma ina ba ku tabbacin cewa; na ci gaba da yin aiki da hukumomin tsaro, domin a bai wa wadannan gonaki kariyar da ta kamata daga wadannan marasa kishin, musamman domin wadanda za su amfana, su yi aiki a cikin gonakin, ba tare da fuskantar wata barazana ko yin garkuwa da su ba,” in ji Oyebanji.

Shi ma a nasa jawabin a wajen taron, kwamishinan ma’aikatar aikin gona da samar da wadataccen abinci na jihar, Mista Ebenezer Boluwade ya bayyana cewa; kimanin manoma 200 ne za su iya yin noma a gidan gonar ta Eporo Ekiti, wadda kuma aka samar mata da kayan aiki na zamani da suka hada da na’urorin samar da hasken wuta ta sola da sauran makamantansu.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *