APC Na Dab Da Mallakar Jihohi Sama Da 30

[ad_1]

Jam’iyyar APC na ƙara kusantar mallakar jihohi sama da 30 cikin 36 na ƙasar nan, bayan ficewar Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, daga jam’iyyar PDP da kuma alamun shirin Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, na barin NNPP. Komawar Mutfwang kaɗai zata, za ta ƙara adadin gwamnonin APC zuwa 28, lamarin da ke nuna gagarumar ƙaruwa idan aka kwatanta da bayan zaɓen 2023.

Rahotanni sun nuna cewa Gwamnan Kano na dab da yin rajista da APC, wanda hakan ka iya kai adadin jihohin da jam’iyyar ke mulki zuwa 29, yayin da wasu gwamnoni daga Zamfara da Abia ke nazarin sauya sheƙa. Masana siyasa sun bayyana cewa wannan yawaitar sauya jam’iyya na faruwa ne sakamakon raunin haɗin kai da rikice-rikicen cikin gida da ke addabar jam’iyyun adawa.

  • Ba Mu Da Shirin Mayar da Nijeriya Ƙasa Mai Jam’iyya Ɗaya – APC
  • Gwamna Abba Ya Kammala Shirye-shiryen Komawa APC A Ranar Litinin

Gwamna Mutfwang ya bayyana cewa sauya sheƙarsa na da nasaba da burinsa na shugabanci mai ma’ana, da aiwatar da ingantaccen aiki ga jiharsa, yana mai cewa APC ta fi dacewa da manufofin ci gaban Jihar Filato da na gwamnatin tarayya.

Masana sun yi gargaɗi cewa yawaitar sauya sheƙa zuwa APC na iya jefa Nijeriya cikin yanayin mulkin jam’iyya guda, wanda hakan ka iya raunana adawa da rage sa ido kan gwamnati.

Duk da haka, APC ta musanta zargin, tana mai cewa karɓar ƴan siyasa daga sauran jam’iyyu abu ne da ke cikin tsarin dimokuraɗiyya.

Duk idanu yanzu suna kan yadda wannan sauyi zai shafi siyasar ƙasar gabanin zaɓen 2027.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *