NiDCOM Ta Nemi A Saki ‘Yan Nijeriya 42 Da Ake Tsare Da Su A Mozambikue

[ad_1]

Shugabar kuma Babbar Daraktar Kungiyar ‘yan Nijeriya Mazauna Kasar Waje, (NiDCOM), Abike Dabiri-Erewa, ta yi Allah-wadai da rahoton kama ‘yan Nijeriya 42 a kasar Mozambikue ba tare da gabatar musu da wata tuhuma a hukumance ba, tana mai bayyana lamarin a matsayin abin damuwa da kuma abin da ba za a amince da shi ba.

Dabiri-Erewa ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a Abuja ta hannun Daraktan Yada Labarai, Hulda da Jama’a da Kuma Tsare-tsare na Hukumar, Abdur-Rahman Balogun.

  • Yawan Dazuzzuka Da Filin Ciyayi a Kasar Sin Ya Wuce Kashi 56%
  • Sin Ta Himmatu Wajen Raya Ci Gaban Duniya Na Bai Daya

Ta nuna damuwa cewa an zargi jami’an tsaro da ware ‘yan Nijeriya ne kadai domin kamawa a cikin wasu ‘yan kasuwa da ke kasuwancin kayan gyaran motoci (spare parts).

A cewarta, abin takaici ne yadda aka ce an ware ‘yan Nijeriya kadai aka kama tare da tsare su ba tare da wani bayani daga hukumomi ba.

Shugabar kungiyar, Abike Dabiri-Erewa, ta ce idan har wasu daga cikin wadanda aka kama sun karya dokokin Mozambikue, to ya kamata a tuhume su a hukumance sannan a gurfanar da su a gaban kotu mai iko.

Ta kara da cewa kamun da aka yi musu ba zato ba tsammani tare da ware su musamman yana tayar da damuwa kan yiwuwar nuna kiyayya ga baki (denophobia) ga ‘yan Nijeriya da ke zaune a kasar.

Saboda haka, ta bukaci hukumomin Mozambikue da su saki wadanda aka tsare nan take, ko kuma su tabbatar an bi dukkan matakan doka yadda ya kamata.

Rahotanni sun nuna cewa an ware ‘yan Nijeriyar ne aka kama a kasuwar kayan gyaran motoci (spare parts) duk da cewa akwai ‘yan kasuwa daga wasu kasashe daban-daban a wurin.

An kuma ce mutanen da aka kama suna zaune a Mozambikue bisa ka’ida, yayin da aka ruwaito cewa Babban Lauyan kasar bai ma san da wata tuhuma da aka shigar a kansu ba.

Har ila yau, an yi zargin cewa an ci zarafin wasu daga cikin wadanda aka kama yayin aikin, tare da kwace musu kayayyakinsu na kashin kai. An kuma ce wasu daga cikinsu sun kamu da rashin lafiya kuma suna bukatar kulawar likita cikin gaggawa.

Dabiri-Erewa ta bukaci hukumomin Mozambikue da su mutunta hakkoki da martabar ‘yan Nijeriya da ke kasar, tare da tabbatar da cewa adalci da gaskiya sun yi rinjaye.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *