Amurka Ce Tushen Matsalar Da Ake Ciki Dangane Da Batun Nukiliyar Iran

[ad_1]

Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Fu Cong, ya ce Amurka ce tushen matsalar da ake ciki yanzu haka dangane da batun nukiliyar kasar Iran, kuma matakan da ta dauka sun saba wa dokokin kasa da kasa, da ka’idojin dake kunshe cikin kundin kafuwar MDD.

Fu Cong, wanda ya bayyana hakan a jiya Alhamis, yayin zaman kwamitin nazarin takunkuman da aka kakabawa kasar Iran na kwamitin tsaron MDD, ya ce Sin na matukar adawa da matakan da Amurka ta aiwatar.

Jami’in ya kara da cewa, wajibi ne a martaba ikon mulkin kai, da tsaro da hurumin yankunan kasar Iran, kuma Amurka da Isra’ila su gaggauta dakatar da aiwatar da matakan soji.

Ya ce dole ne a yi kokarin warware batun nukiliyar Iran ta hanyar siyasa da diflomasiyya, kana a kare ikon Iran na cin gajiyar makamashin nukiliya ta hanyar lumana, a matsayinta na daya daga kasashe da suka amince da yarjejeniyar kasa da kasa ta hana yaduwar makaman nukiliya.

Kazalika, bai kamata kwamitin tsaron MDD ya zamo makamin kakaba takunkumai, matsin lamba, ko dandalin aiwatar da ajandar siyasa ta wasu daidaikun kasashe ba. (Saminu Alhassan)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *