Atiku Ya Yi Murna, Ya Yi Marhaba Da Peter Obi A ADC

[ad_1]

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya yi maraba da sanarwar da tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, ya yi a hukumance, ta sauya sheka daga Jam’iyyar LP zuwa ADC, inda ya bayyana ci gaban a matsayin wani muhimmin lokaci a tarihin kawancen siyasa a Nijeriya.

Atiku ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook, inda ya nuna kyakkyawan fata cewa, shigar Obi cikin ADC zai karfafa siyasar adawa da kuma shimfida harsashi ga gwamnati mai iya samar da wadata da zaman lafiya ga ‘yan Nijeriya.

“Yau ta zama wata muhimmiyar rana a tarihin kawancen siyasa a kasarmu, inda dan uwana kuma abokin tarayya, Peter Obi, a hukumance ya koma cikin Jam’iyyar ADC,” in ji Atiku.

Tsohon dan takarar shugaban kasa na PDP ya ce yana farin cikin maraba da tsohon dan takarar shugaban kasa na LP Obi a hukumance cikin jam’iyyar, yana mai jaddada cewa hadin gwiwarsu zata taimaka wajen samar da “Jam’iyyar adawa mai karfi” wadda za ta iya kalubalantar jam’iyya mai mulki yadda ya kamata kuma ta bai wa ‘yan Nijeriya tukuici da aka dade ana tsumayi a fadin kasar.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *