Jagororin Kasar Sin Sun Halarci Bikin Gala Na Sabuwar Shekara Da Ya Kunshi Wasan Opera Na Gargajiya

[ad_1]

Jagororin kasar Sin sun halarci bikin nishadantarwa na gala na sabuwar shekarar 2026 wanda ya kunshi gudanar da wasan kwaikwayo na opera na gargajiya a jiya Talata da yamma a birnin Beijing.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, da sauran shugabannin jam’iyya da na kasar, ciki har da Li Qiang, Zhao Leji, Wang Huning, Cai Qi, Ding Xuexiang, Li Xi da Han Zheng, sun kalli wasan a Cibiyar Gudanar da Wasannin Nishadantarwa ta Kasa, tare da sauran mutane daga dukkan fannonin rayuwa.

Bikin galar ya kunshi wasu daga cikin wasannin opera na gargajiya da na sabbin da aka kirkiro masu kyau wadanda ke nuna ci gaban da aka samu ta mabambantan fuskoki a wasan opera na gargajiyar kasar Sin mai ban sha’awa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *