Abubuwa 17 Da Suke Lalata Aure (1)
[ad_1]
- Kishi Mai Tsanani: Idan kishi ya yi tsanani sai ya zama matsala ga mai shi da kuma wanda ake kishin a kansa.
- Sa Ido da bibiya: Sa’ido muguwar sana’a, duk wanda ya sa maka ido, yake bibiyar ka, yake neman aibinka ko kuskurenka ko kasawarka, ko laifinka, wannan ba masoyinka bane na gaskiya.
- Matar Da Ta Haifi ‘Ya’ya Hudu Lokaci Guda Na Tsaka Mai Wuya A Kano
- CMG Ya Kammala Bita Zagaye Na Uku Ta Shagalin Murnar Shiga Sabuwar Shekarar Gargajiya Ta Kasar Sin
- Nuna fifiko da isa kan juna: Nuna fifiko da isa, yana jawo raini, da wulaksanci, da rashin kimantawa, babu kuwa mai son a wulakanta shi, duk son da ma’aurata, miji ko mata ya raina abokin zamansa, to zama ba zai yiyu ba a wannan hali, dole a sami cikas.
5 Yawan zargi: Yawan zargi ba tare da dalili ba, yana rushe kauna, da aminci tsakanin ma’aurata, daga nan sai dangantaka ta yi tsami har ta kai ga rushewar aure.
- Cin Amanar aure: Cin amanar aure, daga miji ko mata, yana cikin manyan matsaloli da suke jawo mutuwar aure, da rashin yarda da juna ko da kuwa, mai aikata haka ya tuba.
- Sukurkucewar alaka da Allah: Yawan sabo da kin bin umarnin Allah, yi-na-yi bari-na-bari, yana tasiri wajen rashin jin dadin zamantakewa ta aure, domin sabon Allah yana cire albarkar aure, da jin dadinsa, akwai wani cikin ma gabata yana cewa idan muka saba wa Allah ta’alah, muna ganin sakamakon haka a cikin iyalanmu.
- Son duniya mai tsanani: Mugun son duniya da rashin daukar aure a matsayin kauna ta gaskiya da amana, ba don neman wani abu ba, yana lalata zaman aure, idan bukata ba ta biya ba.
- Bayyana sirrin aure ga kawaye ko abokai: Rashin boye sirrin juna tsakanin ma’aurata, yana kawo cikas da tabarbarewar aure da sakwarkwacewarsa.
- Bangaran Ibada: Rashin ilmin addini da rashin kula da ibada musamman Sallah.
- Munin hali: Munanan halaye da rashin zaman lafiya yana sawa kowa ya gaji da abokin zamansa har ya zama yana fatan a sami dalilin da zai raba ko mutuwar aure ko mutuwar abokin zaman dungurungun.
Za Mu Ci Gaba Mako Mai Zuwa Idan Allah Ya Kai Mu
[ad_2]
Source link