Gwamnan Jigawa ya karɓo Walida daga hannun DSS
Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya karɓo Walida Abdulhadi Ibrahim daga hannun Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS), biyo bayan kiranye-kiranye da jama’a suka dinga yi a kanta.
Aminiya ta ruwaito yadda Walida ta ɓace daga gidansu, wanda iyayenta daga baya suka zargi wani jami’in DSS da sace ta.
Ana zargin jami’in na DSS da aurenta, inda ta haihu a hannunsa tare da tilasta mata sauya addininta daga Musulunci zuwa Kiristanci.
Tun bayan ƙorafin da iyayen suka shigar, yarinyar ta shafe kwanaki a hannun hukumar.
Lokacin da gwamnan ya karɓe ta, ya ce duk zarge-zargen da ake yi wa jami’in hukumar, za a kai su gaban kotu domin a bi su ta hanyar doka, tare da tabbatar da cewa an yi wa kowa adalci.
Ya kuma bayyana cewa Walida ’yar asalin Jigawa ce, kuma gwamnati za ta kula da tsaronta tare da taimaka mata ta samu sauƙi daga duk wata damuwa da ta fuskanta.
Gwamnan ya je hedikwatar DSS da ke Abuja tare da wasu manyan jami’an Gwamnatin jihar, ciki har da kakakin majalisar dokoki, babban lauyan jihar, Kwamishiniyar harkokin mata da sauransu.