Mata Ne Ke Rike Da Kaso 40 Na Matsakaitan Sana’oi —Hannatu Musawa
Masu ruwa da tsaki, a fannin hada-hadar kudi a kasar nan, sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta samar da tsari, domin a dakile shingen da ke hana matan kasar shiga a dama da su, a fannin tattalin arzikin kasar nan.
Sun yi gargadi da cewa, duk da cewa, matan kasar ne ke da kaso 40 a cikin dari na matsakaita da kananan sana’oin amma har yanzu, suna ci gaba da fuskantar gibi ne samun rancen kudaden da za su ci gaba da bunkasa kasuwancin su.
- INEC Ta Gyara Jadawalin Zaben 2027 Tare Da Tsawaita Wa’adin Mika Rajistar Jam’iyyun Siyasa
- NPA Ta Kaddamar Da Tsarin Kara Bunkasa Fitar Da Kayan Da Basu Da Nasaba Da Fannin Mai
Ministar al’adu da kirkirar tattalin arziki Hannatu Musawa da kuma tsohuwar ministar ilimi Oby Ezekwesili, suka bayyana wannan damuwar a jawabinssu da ban da ban a taron ranar mata ta duniya na bana, na wannan shekarar da aka gudanar a kwananbaya a jihar Legas.
Sun zayyano kalubalen da mata masu gudanar da kanana da matsakaitan sana’oin ke ci gaba da fuskanta wajen samun rancen kudaden daga bankuna da cibiyoyin hada-hadar kudade, na kasar nan wanda hakan ke janyo masu na shiga a dama da su, a fagen kara ciyar da tattalin arzikin kasar gaba..
Musawa ta yi nuni da cewa, har yanzu matan kasar nan, su ne a kan gaba a,fannin bunkasa tattalin arzikin kasar nan, amma abin takaici, suna ci gaba da fuskantar kalubale na samun kudaden da za su ci gaba da gudanar da kasuwancin su.
Ta kara da cewa, hakan na kuma dakile su, daga samun damar kara fadada kasuwanin su,inda ta yi nuni da cewa, hakan,babbar koma baya ne, ga kasuwanin su.
Sai dai, a bangaren gwamatin tarayya, ministar ta bayyana cewa, domin a magance wannan matsalar na ci gaba da samar da shirye-shiye, bisa nufin samar wa da mata’yan kasuwa kudaden da za su ci gaba da bunkasa kasuwancin su, musamman ta hanyar ma’aikatar da take shugabanta.
Ta jaddada cewa ,akwai bukatar a sanya mata a kasar a cikin batun gudanar da tsare-tsare da kuma daukar matakan bayar da shawara, musamman duba da fahimtar al’amuran yau da kullum da su ke da shi, a bangaren gudanar da shugabanci da kuma shuganci, a bangaren tafiyar da tattalin arzikin kasar.
Ita kuwa a na ta jawabin tsohuwar ministar ta ilimi ta bayyana cewa, shigen da ke dakile matan’yan kasuwa na kasar nan na haifar da gagarumin cikas wajen bayar da gudunmawar su, a fagen kara bunkasa fannonin tattalin arzikin kasar
Ta buga misali kan hujjar yadda a kasashen duniya, ake samarwa da mata ‘yan kasuwa, kudaden da suke ci gaba da habaka sana’oin su,wanda hakan, ke kara habaka fannin tattalin arzikin kasashen.
A cewar tsohuwar ministan magance wannan matsalar, ba wai kawai ta tallawa sana’oin su aka yi ba, har da kuma kara karfafa fannin tattalin arzikin kasar da kuma bayar da damar, gudanar da yin gasa, a fannin kasuwanin kasar.
“Akwai bukatar a kawar da wannan shingen da janyo mata ‘ yan kasuwa na kasar samun kudaden da za su bunkasa kasuwancin su, inda hakan zai ba su damar kara fadada kasuwancin su.
Ta buga misali da fannin aikin noma wanda ta bayyana cewa, muna gsni kaso 30 a cikin dari matan da suka rungumi fannin na bayar da gagarumar gudunmawa,” .Inji tsohuwar ministan.
Ta alakanta wannan matsalar ta gibin na ssmun kudaden ga matan’yan kasuwa, a matsayin babban abin da ke taka masu birki a fagen kasuwancin su.
Ta yi gargadi da cewa, ci gaba da barin wannan gibin, za a ci gaba da dakile matan ‘yan kasuwa na kasar daga bayar da ta su gudunmawar wajen ciyar da tattalin arzikin kasar gaba.
Ta kuma bayar da shawarar da a yi hadaka a tsakanin masana’antu masu zaman kansu da kuma masu kirkiro da dokoki a kasar domin a janyo matan kasar ‘yan kasuwa domin a rinka tattaunawa da su a fannin tattalin arzikin kasar.