’Yan bindiga sun sace uwa da ’ya’yanta mata 4 a Kaduna
[ad_1]
’Yan bindiga sun sace wata mata da ’ya’yanta mata huɗu a ƙauyen Kurmin-Uwa kusa da garin Janjala a Ƙaramar Hukumar Kagarko ta Jihar Kaduna.
Wannan harin ya faru ƙasa da sa’o’i 24 bayan wani hari da wasu mahara suka kai Unguwar Sabon-Titi, Katari, inda aka sace mutum bakwai ’yan gida ɗaya, da maƙwabtansu uku.
Wani mazaunin yankin, Ibrahim Shehu, ya ce harin na baya-bayan nan ya faru da misalin ƙarrfe 10:23 na daren ranar Juma’a.
Ya bayyana cewa maharan sun nufi wani gida kai-tsaye kuma suka tafi da mutane bakwai.
Ya bayyana sunayen waɗanda aka sace da suka haɗa da Ladi Malachy, Patience Malachy, Promise Malachy, Inama Malachy, Peter Malachy da Aboyi Malachy.
Wani shugaban jama’a a yankin ya tabbatar da aukuwar harin.
Ya ce nan take ya sanar da jami’an tsaro bayan samun kiran gaggawa.
“Da na samu kiran gaggawa cewa ’yan bindiga sun shiga ƙauyen Kurmin-Uwa, nan take na sanar da jami’an tsaro, amma ban san ko sun kai ɗauki ba,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa ƙauyen yana da nisan kilomita biyu daga garin Kagarko, kuma al’ummar yankin na cikin damuwa kan yawaitar hare-haren ’yan bindiga.
“Har yanzu ba a tuntuɓi masu garkuwa da mutanen ba, kuma hare-haren na ƙara yawaita a wannan yanki,” in ji shi.
Wani jami’in tsaro ya ce bai da labarin sabon harin, amma zai bincika.
“Tun ranar Talata muna cikin daji muna neman maɓoyar ’yan bindiga a yankin Kachia domin ceto waɗanda aka sace a baya, amma zan bincika wannan labarin,” in ji shi.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Hassan Mansur, bai amsa kiran waya ko saƙon da aka aike masa ba dangane da harin.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link