Rikicin ADC: Lauya Ya Caccaki Kotun Ɗaukaka Ƙara

[ad_1]

Wani lauya mai zaman kansa a birnin Legas, Liborous Oshoma, ya yi tsokaci mai zurfi kan rikicin shugabanci da ke addabar jam’iyyar ADC, inda ya bayyana cewa hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke ya ƙara rikita al’amura maimakon warware su, musamman dangane da umarnin da ta bayar na a ci gaba da bin tsarin “status quo ante bellum” duk da cewa ta kori ƙarar da aka shigar a gabanta.

Oshoma, a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa tushen rikicin ya samo asali ne daga ƙarar da Nafiu Bala Gombe ya shigar a Babbar Kotun Tarayya, inda yake neman a fassara kundin tsarin mulkin jam’iyyar ADC domin tabbatar da iƙirarinsa na shugabanci bayan murabus ɗin tsohon shugaban jam’iyyar, lamarin da ya haifar da cece-kuce tsakanin ɓangarori daban-daban na jam’iyyar.

  • Komawar Kwankwaso ADC, Zai Jawo Hankalin Manyan ‘Yan Siyasa Zuwa Jam’iyyar
  • Kano Pillars Sun Yi Alƙawarin Sake Zage Damtse Bayan Rashin Nasarar Wasan Bayelsa

Ya ƙara da cewa, bayan kotun farko ta ƙi amincewa da bukatar bayar da umarnin gaggawa (ex parte), sai ta bukaci a sanar da sauran ɓangarori su zo su kare kansu, amma wannan mataki bai yi wa Sanata David Mark daɗi ba, wanda ya garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara domin ƙalubalantar matakin, sai dai kotun ta ƙi sauraron ƙarar bisa rashin samun izini (leave) daga kotu kamar yadda doka ta tanada.

Sai dai duk da korar ƙarar, Oshoma ya nuna damuwa kan yadda Kotun Ɗaukaka Ƙara ta sake bayar da umarni ga ɓangarorin da su ci gaba da bin tsarin da ake ciki, yana mai cewa wannan mataki na iya haifar da rikice-rikicen fassara da kuma ruɗani a tsakanin masu ruwa da tsaki, maimakon samar da mafita mai ɗorewa ga rikicin da ke addabar jam’iyyar.

A cewarsa, mafi dacewa shi ne kotun ta umurci ɓangarorin da su nemi a hanzarta sauraron babbar shari’ar a Babbar Kotun Tarayya, musamman duba da muhimmancin lokaci yayin da ake tunkarar zaɓen 2027, yana mai jaddada cewa jinkiri a irin wannan lamari na iya kawo tangarda ga tsarin dimokuraɗiyya da kuma shirye-shiryen zaɓe a ƙasar.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *