Tashar ajiye manyan motoci za ta samar wa matasa 5,000 ayyuka a Yobe – Kwamishina

[ad_1]



An bayyana cewa, tashar ajiye manyan motocin ɗaukar kaya da Gwamnatin Jihar Yobe ta gina a garin Potiskum kan iya samar da guraben ayyuka ga matasa dubu 5 da zarar an buɗe ta.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Kwamishinan Ma’aikatar Harkokin Cikin gida, Yaɗa Labarai da Al’adu na Jihar Yobe, Alhaji Abdullahi Bego a lokacin ziyarar duba aiki da manema labarai ke yi, inda ya bayanna cewa, sabon wurin ajiye motoci na Potiskum zai bai wa matasa marasa aikin yi 5,000 guraben aiki a yankin na Potiskum.

Wannan sanarwar ta nuna irin jajircewar Gwamna Mai Mala Buni na haɓaka aikin yi a yankin da kuma fahimtar muhimmiyar rawar da al’umma ke takawa a fannin sufuri da kuma ƙera bodin motocin tirela.

Gwamna ya gina tashar motocin tirela ta zamani don rage cunkoso a garin Potiskum, wanda shi ne cibiyar kasuwancin jihar.

Tashar ajiye manyan motocin na gab da kammaluwa, inda ta ƙunshi manya-manyan wuraren ajiya (stores) guda biyu da rijiyoyin burtsatse da dama da masallaci da sashin kashe gobara da ofishin ‘yan sanda da kuma filin ajiye motoci mai faɗin mita 86,000, wanda zai iya ɗaukar manyan motoci 500 a lokaci guda.

A cikin jawabinsa Kwamishinan Gidaje, Ahmed Buba ya ce, wannan wurin ajaiyar manyan motocin ya ƙunshi hanyoyi masu kyau da otel don baƙi da ‘yan kasuwa.

Daga baya, kwamishinan ya kuma jagoranci manema labaran zuwa garin Ngalda, a kan titin Gombe, inda Gwamnatin Buni ta gina kasuwa ta zamani a matsayin ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin kasuwanci na Yobe.

Da yake jawabi, Hakimin Gundumar Ngalda, Alhaji Danbaba Ngalda, wanda Wakilinsa Alhaji Ahmadun Kano ya wakilta, ya yaba wa Gwamnatin Jihar Yobe bisa samar da wannan sabuwar kasuwa ta zamani a kan iyaka.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *