FERMA ta ƙaddamar da aikin gyara tsohuwar hanyar Kano

[ad_1]



Hukumar kula da gyaran manyan hanyoyi ta ƙasa (FERMA) reshen Jihar Kaduna, ta ƙaddamar da aikin gyaran tsohuwar hanyar Zariya zuwa Makarfi wadda ta haura zuwa Kano.

Aikin zai haɗa da tono ciyayi, cike ramuka, da yashe magudanan ruwa tare da samar da ayyukan yi na wucin gadi ga matasa da ke yankin.

Da yake ƙaddamar da shirin a Basawa, Zariya, shugaban FERMA na jihar Kaduna, Injiniya Kabir Iliyasu Danmarke, ya bayyana cewa aikin umurni ne daga shugaban hukumar na ƙasa, Dr. Chuku Emeka Obasi, bisa kudurin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na rage haɗurra a hanyoyi.

“Mun ɗauki matasa 50 da za su yi aikin nan cikin wata guda, kuma akwai yiwuwar ƙara wa’adin idan bukata ta taso,” in ji shi.

Danmarke ya ce aikin da aka sanya masa suna “Operation Safeguard of Road” na nufin rage haɗurra da ke faruwa sakamakon tsawon ciyayi a gefen hanya da kuma lalacewar hanya.

Ya ƙara da cewa aikin zai rage kuɗin da direbobi ke kashewa wajen gyaran motoci, tare da samar da aikin yi ga matasa masu shekaru 18 zuwa 45 daga yankin domin inganta rayuwarsu.

Shugaban hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) mai kula da yankin Zariya, Nasir Abdullahi Falgore, ya ce aikin ya zo a daidai lokacin “Ember Months” — watannin ƙarshen shekara da ake yawan zirga-zirga.

Ya yaba da shirin FERMA tare da kiran a ci gaba da irin wannan aiki a sauran hanyoyi.

Haka kuma, wakilin rundunar ‘yan sanda na Samaru, Zariya, ya yi alkawarin samar da tsaro ga ma’aikatan da ke gudanar da aikin domin tabbatar da an aiwatar da shi yadda ya kamata.

Aminiya ta ruwaito cewa a wajen ƙaddamarwar, an raba kayayyaki ga ma’aikatan da aka ɗauka domin sauƙaƙa gudanar da aikin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *