IMF Ya Daga Alkaluman Hasashen Bunkasar Tattalin Arzikin Sin

[ad_1]

Asusun bayar da lamuni na IMF, ya daga alkaluman hasashen bunkasar tattalin arzikin kasar Sin na shekarar 2025 da kaso maki 0.2, zuwa kaso 5 bisa dari, yayin da ya ce alkaluman hasashen na shekarar 2026 da muke ciki, za su wanzu. Kana asusun ya daga alkaluman hasashen ci gaban tattalin arzikin duniya na bana da kaso maki 0.2 zuwa 3.3 bisa dari, idan an kwatanta da hasashen watan Oktoban shekarar da ta shude.

Asusun IMF ya bayyana hakan ne cikin rahotonsa na hasashen bunkasar tattalin arzikin duniya, wanda ya fitar a Litinin din nan. Ya kuma alakanta karuwar alkaluman hasashe kan kyautatuwar sassan raya tattalin arzikin manyan kasashe irin su Amurka da Sin.

Rahoton ya kuma ce karuwar zuba jari a fannin fasahohin sadarwa, wanda ke samun tagomashi daga bunkasar bangaren kirkirarriyar basira ko AI, na cikin muhimman ginshikai dake ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *