[ad_1]
A daidai lokacin da ake ta rade-radin sauya shekarsa, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gana da Shugaba Bola Tinubu a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja a yammacin yau Litinin.
Tattaunawar wacce ke gudana a sirrance, ta kara rura wutar jita-jitar cewa gwamnan, wanda aka zaɓa a karkashin jam’iyyar NNPP, yana shirin komawa jam’iyyar APC mai mulki.
- Adalci: Gwamnatin Kano Ta Karɓi Ragamar Shari’ar Kisan Uwa Da ‘Ya’yanta 6
- AFCON 2025: Morocco Ta Nemi A Binciki Barazanar Katse Wasa Da Senegal Ta Yi
Duk da cewa, akwai rahotannin da ke cewa, batun sauya shekar ta fuskanci cikas, bayan kin amincewa da bukatar gwamnan na bashi tikitin takara kai tsaye kafin zaben gwamna na 2027 a jihar Kano.
A halin yanzu, shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Rabiu Kwankwaso, ya yi watsi da ikirarin cewa ya amince da duk wani shirin sauya sheka da gwamnan ke yi, yana mai tabbatar da cewa, bai da wata masaniya kan shirin gwamnan na ficewa.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, ana kan ci gaba da tattaunawar a lokacin hada wannan rahoton.
[ad_2]
Source link