Tinubu ya karrama abokinsa Gilbert Chagoury da lambar girmamawa

[ad_1]



Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karrama wani tsohon abokin hulɗarsa a harkar kasuwanci, Gilbert Chagoury, da lambar girmamawa ta Grand Commander of the Order of the Niger (GCON), wadda ita ce ta biyu mafi girma a Najeriya.

Tinubu ya ce an ba Chagoury lambar ne bisa gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban ƙasar nan.

A wasiƙar bai wa Chagoury lambar yabon da ke yawo a shafukan sada zumunta, ta bayyana cewa an yi karramawar ne domin yaba wa kyawawan halayensa da ayyukansa a Najeriya.

Da yake martani, attajirin ɗan kasuwar nan, Femi Otedola, ya bayyana cewa bayar karramawar da aka yi wa Chagouri an sanya ƙwarya a gurbinta.

Otedola ya kuma yaba wa Chagoury kan rawar da ya taka a manyan ayyukan gine-gine da bunƙasa birane kamar Banana Island da Eko Atlantic City a Legas, waɗanda suka samar da ayyukan yi da ci gaba mai ɗorewa.

Chagoury wanda ɗan asalin ƙasar Lebanon ne amma haifaffen Jihar Legas, shi ne ya kafa  rukunin kamfanin Chagoury Group tare da ɗan uwansa Ronald a 1971, kamfani da ke da hannun jari a fannoni da dama ciki har da gine-gine, gidaje, masana’antu, sadarwa da fasaha.

Ana iya tuna cewa, a shekarar 2024 aka yi ta ce-ce-ku-ce bayan gwamnatin Tinubu ta ba kamfanin Hitech mallakin Chagoury aikin titin Legas zuwa Calabar kan kuɗi dala biliyan 11, a sakamakon rashin bai wa jama’a dama ta neman kwangilar.

Haka kuma, rahotanni sun nuna cewa ɗan shugaban ƙasa, Seyi Tinubu, na da alaƙar kasuwanci da iyalan Chagoury.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *