Sauya Sheƙar Gawuna Zuwa ADC Babban Koma Baya Ne Ga APC – Bashir Ahmad
Bashir Ahmad, tsohon hadimin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, ya ce ficewar Nasiru Gawuna daga APC zuwa ADC babban rashi ne ga jam’iyyar.
A wani saƙo da ya wallafa a Facebook, Ahmad ya ce Gawuna jigo ne a APC, kuma rasa shi zuwa jam’iyyar adawa babban koma baya ne.
- ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Wajen Biki A Kaduna, Sun Kashe Mutane 13
- Sojoji Sun Kama Mutane 58 Kan Haƙar Ma’adanai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Edo
Gawuna, tsohon mataimakin gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar gwamna na APC a zaɓen 2023, ya yi murabus daga muƙaminsa na shugaban Hukumar Bankin Gidaje ta Tarayya (FMBN).
Ya ce ya yi hakan ne domin bin umarnin da ke buƙatar masu riƙe da muƙaman siyasa su sauka bisa dokar zaɓe.
Ana sa ran zai kammala sauya sheƙa zuwa ADC nan ba da jimawa ba, yayin da sauye-sauyen siyasa ke ƙara ƙamari a Kano.
Gawuna ya gode wa Shugaba Bola Tinubu bisa damar da ya ba shi ya yi aiki, sannan ya ce a shirye yake ya miƙa ragamar aikinsa yadda ya kamata.
Ya kuma ce yana roƙon Allah Ya ɗora shi a tafarki madaidaici a matakinsa na gaba.