El-Rufai Ya Koma Kotu Bayan Rasuwar Mahaifiyarsa

[ad_1]

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya koma Kotun Tarayya da ke Kaduna, inda ake sa ran za a saurari buƙatar ba da belinsa.

Hukumar ICPC ta gurfanar da shi a kotu kan tuhume-tuhume guda 10, ciki har da zargin karkatar da kadarorin gwamnati da kuma almundahanar kuɗaɗe.

  • Sauya Sheƙar Gawuna Zuwa ADC Babban Koma Baya Ne Ga APC – Bashir Ahmad
  • Gawuna, Ya Yi Murabus Daga Shugabancin Hukumar FMBN Gabanin Shiga ADC

El-Rufai ya bayyana a gaban kotu bayan shafe sama da wata guda a tsare.

Tun da farko, kotun ta sanya ranar 31 ga watan Maris, 2026 domin sauraron buƙatar bayar da belinsa.

An sake shi a ranar 27 ga watan Maris bisa dalilai tausayawa, bayan rasuwar mahaifiyarsa a birnin Cairo na ƙasar Masar.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *