An kama wanda ake zargin dan kungiyar ISWAP ne a Maiduguri

[ad_1]



Sojoji sun kama wani da ake zargi da zama dan kungiyar Boko Haram ne a Jihar Borno yayin da yake yunkurin kutsawa cikin garin Maiduguri.

Majiyoyi sun bayyana cewa an kama wanda ake zargin, da aka fi sani da Saina ne da misalin qarfe 4:42 na yamma a ranar 29 ga Maris a wani shingen bincike a yankin Kilo Papa.

Sojojin rundunar 21 ta musamman da jami’an tsaro da aka tura a wurin binciken ne suka kama shi.

A cewar majiyoyin, an kama shi ne yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Maiduguri a cikin wata motar fasinja kuma an same shi sanye da wando irin na kakin sojoji, wanda hakan ya haifar da shakku dangane da lamarinsa.

Majiyar na cewar alamomin farko na nuna cewa wanda ake zargin da farko ya yi ikirarin cewa shi mamba ne na rundunar hadin gwiwa ta sojoji da ke aiki a Kumshe.

Daga bisani da bincike ya yi zurfi sai aka gano cewar, mamba ne na wata qungiyar ta’addanci kuma ana zargin yana kan aikin leken asiri ne a lokacin da aka damke shi.

Tunin an mika wanda ake zargin ga jami’an leken asiri na soja don fadada bincike akan sa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *