An yi wa limami yankan rago da garkuwa da mutane 100
[ad_1]
Wani harin da ake zargin ’yan ta’addar Boko Haram/ISWAP ne suka kai, garin Ngoshe cikin ƙaramar hukumar Gwoza ta jihar Borno sun kashe wani limamin masallaci ta hanyar yi masa yankan rago yayin da suka kwashe mutane sama da 100 da suka haɗa da mata da ƙananan yara.
Majiyoyin tsaro sun ce, ’yan ta’addan sun kai harin ne a ranar Talata, jim kaɗan bayan mazauna garin sun yi buɗa baki a wannan watan Ramadan mai alfarma ga al’ummar Musulmai.
Wata majiyar tsaro, wacce ta yi magana ba tare da an ambaci sunanta ba saboda ba a ba ta izinin yin magana a bainar jama’a ba, ta shaida cewa maharan sun isa wurin da yawa kuma ɗauke da makamai.
A cewar majiyar, ’yan ta’addan sun mamaye sansanin sojojin da ke yankin da ƙarfin bindiga a lokacin harin duk da cewar ana zaton a nan ma ‘yan ta’addan sun kashe wasu sojojin da ake tsammanin sun kai tara, amma ba a hukuman ce ba.
Majiyar tsaron ta ce maharan sun kai hari ga dukkan al’ummar Ngoshe, inda suka kashe babban limamin tare da sace mata da yara sama da 100, suka raunata mutanen da dama.
‘Yayin da nake magana da ku yanzu, mafi yawan mutanen Ngoshe sun gudu kuma babu wanda ya rage a cikin al’ummar. Yawancinmu mun fake a Pulka,’ in ji majiyar.
Majiya ta ci gaba da zargin cewa, maharan sun sami taimako daga wani mai shiga tsakani a cikin al’umma.
‘Sun zo a shirye suka shiga garin Ngoshe da taimakon wani mai shiga tsakani, suka kashe sojoji 9, suka yanka babban limamin masallacin, sannan suka sace mata da yara sama da 100,’ in ji shi.
Mazauna yankin sun kuma ruwaito cewa maharan sun ƙona wasu sassan garin yayin da suke ja da baya, lamarin da ya tilasta wa mafi yawan mazauna garin suka tsere.
Duk ƙoƙarin da aka yi na jin ta bakin mai magana da yawun rundunar Operation Haɗin Kai, Laftanar Kanar Sani Uba, don jin ta bakinsa a hukumance bai yi nasara ba har zuwa lokacin da aka kammala wannan rahoton.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link