Majalisar Zartarwa Ta Ƙasa Ta Amince Da Biyan Garatutin Ma’aikatan Tarayya 100%

[ad_1]

Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da sabon tsarin alawus na barin aiki wanda zai bai wa ma’aikatan gwamnatin tarayya da suka yi ritaya cikakken kuɗinsu  kashi 100 cikin 100 na jimillar albashinsu na shekara guda. Sabon tsarin zai fara aiki daga ranar 1 ga Janairu, 2026.

Sanarwar ta fito ne daga ofishin Didi Esther Walson-Jack, Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, inda ta bayyana cewa ma’aikatan da suka yi aƙalla shekaru 10 suna aiki za su ci gajiyar shirin, baya ga tsarin fansho na gudummawar ma’aikata da ake aiwatarwa a yanzu.

  • Yadda Za A Magance Ciwon Sanyi (Infection) Da Tafarnuwa
  • Matatar Dangote Ta Ƙara Farashin Fetur, Ta Dakatar Da Lodi

A cewarta, amincewar ta biyo bayan shawarwari da nazari na kwamitin haɗin gwuiwar ma’aikatu, wanda ya haɗa da Hukumar Fansho ta Ƙasa, da Ofishin Kasafin Kuɗi na Tarayya da Ofishin Babban Akanta Janar na Tarayya domin samar da tsarin aiwatarwa mai dorewa.

Walson-Jack ta ce matakin na nuna yadda gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke girmama sadaukarwar ma’aikatan gwamnati, tare da ƙara cewa za a fitar da cikakkun ƙa’idojin aiwatar da shirin nan gaba.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *