An sake samun ƙarin mutuwar wasu a Benuwe

[ad_1]



Gwamnatin Jihar Benuwe ta tabbatar da samun ƙarin mace-mace sakamakon ɓarkewar cutar zazzaɓin Lassa, yayin da jami’an lafiya ke ƙarfafa gwiwa wajen daƙile yaɗuwar cutar a faɗin jihar.

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa, a makon da ya gabata ne gwamnatin jihar ta tabbatar da mutuwar ma’aikatan lafiya 10 biyo bayan ɓarkewar cutar, inda aka samu mutum 45 da suka kamu da cutar daga cikin mutum 250 da ake zargin suna ɗauke da ita a fadin jihar.

Sai dai, Kwamishinan Lafiya da Ayyukan Jin Kai na Jihar, Paul Ogwuche, ya ba da sabbin alƙaluma a ranar Alhamis yayin da yake jawabi a wani taron bita kan Tsarin Ayyuka na Shekara ta 2026 na Kwamitin Yaƙi da Cutar Kanjamau (BENSACA) a garin Makurdi.

Ogwuche ya bayyana cewa jihar ta rubuta samu bayanan mutane 251 da ake zargin suna ɗauke da zazzabin Lassa yayin da ake ci gaba da sanya ido kan ɓarkewar cutar.

Ya bayyana cewa ya zuwa ranar 4 ga Maris, 2026, an tabbatar da mutum 46 sun kamu da cutar, yayin da mutum 11 suka riga mu gidan gaskiya.

A cewar kwamishinan, ma’aikatan lafiya 13 su ma sun kamu da ƙwayar cutar. Ma’aikatan da abin ya shafa sun haɗa da: Likitoci biyar da Masanin harhaɗa magunguna guda ɗaya da Ma’aikatan jinya gudu huɗu da Ma’aikatan lafiya na matakin farko (CHEW) guda biyu. Da kuma ma’aikacin ɗaukar marasa lafiya guda ɗaya.

Ya ƙara da cewa, a halin yanzu akwai marasa lafiya 29 da ke karɓar magani a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Benuwe da kuma Babban Asibitin Tarayya (FMC) da ke Makurdi.

Ogwuche ya ce jami’an lafiya sun ƙarfafa sa ido, rigakafin kamuwa da cutar, da kuma matakan sarrafa ta, tare da wayar da kan al’umma biyo bayan sabbin abubuwan da suka faru game da cutar.

Ya bayyana cewa, ana kamuwa da zazzabin Lassa ne galibi ta hanyar taɓa abinci ko kayan gida da ɓera masu ɗauke da cutar suka taɓa, ko kuma ta hanyar mu’amala da ruwan jikin mutumin da ya riga ya kamu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *