An Ɗage Shari’ar  Ganduje Da Matarsa Saboda Rashin Miƙa Takardu

[ad_1]


An ɗage sauraron shari’ar tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, matarsa Hafsat, da wasu mutum shida a ranar Litinin bayan sun kasa miƙa takardun da ake buƙata a kotu.

Gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da su bisa tuhume-tuhume 11 da suka shafi cin hanci, haɗa baki wajen yin laifi, da karkatar da kuɗaɗen gwamnati da suka kai miliyoyin Naira.

Lokacin da aka fara sauraren shari’ar, lauya mai kare gwamnati, Adeola Adedipe (SAN), ya ce sun shirya fara gabatar da shaidu, amma lauyoyin Ganduje da sauran waɗanda ake tuhuma suka nemi ƙarin lokaci, inda suka bayyana cewar ba a ba su wasu takardu ba.

Alƙalin kotun, Mai Shari’a Amina Adamu-Aliyu, ta umarci dukkanin ɓangarorin su kammala miƙa takardunsu kafin zaman kotun na gaba, sannan ta ɗage shari’ar zuwa 26 ga Nuwamba, 2025.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *