Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 2, Sun Ceto Mutane 62 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kebbi Da Zamfara

[ad_1]

Rundunar Sojojin Hadin Gwiwa Ta ‘Operation FANSAN YAMMA’ sun kashe ‘yan ta’adda 2 a Jihar Kebbi tare da ceto mutane 62 da aka yi garkuwa da su a Dajin Munhaye na Jihar Zamfara.
Sanarwar Mukaddashin Darakta na Hulda da Jama’a na Sojin Nijeriya, Rundunar Sojin Sashe na 8/2 FANSAN YAMMA, Laftanar Kanal Osoba Olaniyi, ya fitar, ya ce, an an gudanar da ayyukan ne tare da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro da ‘yan banga na yankin.
  • Ci Gaban Tattalin Arzikin Kasar Sin Ba Tare Da Tangarda Ba A 2025 Ya Karfafa Gwiwar Kasashe Masu Tasowa
  • Boko Haram Sun Kai Hari Sansanin Sojoji A Borno
Ya ce sojoji a Jihar Kebbi, sun yi amfani da bayanan sirri wajen kai wa ‘yan ta’addan Lakurawa hari kusa da kan iyaka tsakanin karamar hukumar Augie ta Jihar Kebbi da karamar hukumar Binji ta Jihar Sokoto.
Ya ce, samamen da ya gudana a kauyen Kerani, ya yi sanadin kawar da ‘yan ta’adda 2 da kuma kwato babura 2 da ‘yan ta’addan ke amfani da su.
Har ila yau, a Jihar Zamfara, sojoji a wani samame daban, sun kai hari a Dajin Munhaye, a wani sansanin fitaccen dan bindiga, Kachalla Alti bayan rahoton sirri da ke cewa, shugaban ‘yan fashin ya yi garkuwa da wasu mutane a maɓoyar.
“Wannan samamen ya kai ga nasarar ceto mutane 62 da aka yi garkuwa da su, wadanda yanzu haka suna hannun jami’an tsaro,” in ji shi.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *