NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna



Ƙungiyar Lauyoyi ta Nijeriya (NBA) ta nuna rashin jin daɗi game da hukunce-hukuncen da ke karo da juna daga kotuna.

Ƙungiyar lauyoyi ta yi wannan kira ne yayin da take yi wa ‘yan jarida bayani kafin Makon Shari’a na 2025, inda ta kuma yi kira da a yi gyare-gyare don daidaita shari’o’in kafin zaɓen dake tafe a ƙasar.

A cewar reshen Akure na NBA, jam’iyyun siyasa ya kamata su rika fuskantar hukunci na shari’a saboda karya ƙa’idodin dimokuraɗiyya.

Shugaban reshen Akure na NBA, Mr. Friday Umar, wanda ya yi wannan kira, ya lura cewa “wani lokacin, yanke hukuncin masu karo da juna, suna tasowa ne daga bambance-bambancen ra’ayoyin alkalai” kuma ya amince cewa Majalisar Shari’a ta Ƙasa (NJC) tana ƙoƙarin kawo ƙarshen wannan yanayi.

Ya ƙara da gargaɗin cewa, ya kamata a riƙa shigar da ƙara a inda aka yi laifi don kiyaye mutuncin shari’a.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *