Ya kamata duk ɗan Najeriya ya damu da barazanar Trump– Jigon APC

[ad_1]



Wani jigo a Jam’iyyar APC a Jihar Osun, Olatunbosun Oyintiloye, ya ce ya kamata kowane ɗan Najeriya ya damu game da barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi.

Ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu da hukumomin tsaro bisa ƙoƙarinsu na yaƙar rashin tsaro, tare da kiran ’yan Najeriya da su haɗa kai don kare ƙasar.

Oyintiloye, ya ce matsalar tsaro ba a zamanin Tinubu ta samo asali ba, kuma a cewarsa matsalar na shafar addinai daban-daban a ƙasar.

“Dole ne mu tsaya tare da Shugaba Tinubu. Wannan ba lokacin rabuwar addini ko siyasa ba ne. Abin da muke buƙata yanzu shi ne haɗin kai don kare ƙasarmu,” in ji shi.

Ya shawarci ’yan adawa da su yi hattara da kalamansu, tare da kira ga manyan hafsoshin soji da su tabbatar da amincewar da aka ba su ta hanyar yin aiki tuƙuru wajen murƙushe ’yan ta’adda.

Oyintiloye, ya kuma roƙi gwamnatin Amurka da ta taimaka wa Najeriya da bayanan leƙen asiri da kayan yaƙi maimakon turo sojojinta, inda ya ce hakan na iya ƙara dagula lamarin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *