An yi garkuwa da ’yan kwamitin masallaci yayin shirye-shiryen Ramadan a Filato
[ad_1]
Wasu mutum takwas a unguwar Doguwan Ruwa da ke gundumar Bashar a Ƙaramar Hukumar Wase ta Jihar Filato, sun faɗa tarkon masu garkuwa da mutane a yammacin ranar Lahadin da ta gabata.
Mutanen da lamarin ya shafa ’yan kwamitin Masallacin Juma’a ne na Jama’atu Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah (Izala) da ke yankin kamar yadda wani jagoran matasa a Ƙaramar Hukumar Wase, Sapi’i Sambo, ya bayyana a ranar Litinin.
Ya bayyana cewa mutanen da aka sace sun haɗa da limamin masallacin, Abdulrashid Baduku, da kuma ladaninsa, waɗanda ’yan bindiga masu yawa suka kaiwa hari a bayan gari.
Ya ƙara da cewa mutum ɗaya ya rasa ransa yayin harin, lamarin da ya jefa al’umma cikin fargaba, musamman ganin cewa yankin ya kwashe kusan watanni biyar ba tare da tashin hankali ba.
Shi ma Sa’idu Mustafa, wani wanda ya tsira daga hannun ’yan bindigar, ya ce su goma ne gaba ɗaya a lokacin da aka kai harin, kuma dukkansu ’yan kwamitin masallaci ne da ke aikin sarrafa gawayi domin tara kuɗin da za a yi amfani da su wajen ɗaukar malamai da za su gabatar da Tafsirin Alƙur’ani a watan Ramadan.
Da yake ba da labarin abin da ya faru, Mustafa ya ce: “Mu goma ne, duk ’yan kwamitin masallaci.
“Mun haɗa kai muna sarrafa gawayi domin tara kuɗin Tafsirin Ramadan, saboda ba kowa zai iya ɗaukar nauyin aikin shi kaɗai ba.
“Yayin da muke aiki, sai ’yan bindiga ɗauke da makamai suka zo a kan babura, suna harbe-harbe suka tarwatsa mu.
“Mun tarwatsa muka ranta a na kare, amma sai da suka samu nasarar kama mutane takwas, ciki har da limamin masallacin, ladaninsa da sakataren masallacin.
“Sun kuma kashe mutum ɗaya. Ni ne kaɗai na tsira, amma wannan lamarin ne mai matuƙar razani.”
Mustafa ya ƙara da cewa har yanzu mutanen da aka sace suna hannun masu garkuwa da mutane.
Aminiya ta tuntuɓi Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Filato, SP Alabo Alfred, amma hakar ba ta cimma ruwa ba wajen neman tsokacinsa kan lamarin.
Wakilinmu ya ruwaito cewa a watan Yulin 2025, ’yan bindiga sun yi wa sojoji da ’yan sa-kai kwanton ɓauna a wannan unguwar ta Doguwan Ruwa, inda aka kashe sojoji biyu da ’yan sa-kai biyu.
Haka kuma, a Litinin ɗin makon da ya gabata ne ’yan bindiga suka kai hari a unguwannin Sabon Gari da Zak, inda suka kashe mutum biyar da kuma wani soja guda.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link