Shekaru 55 Da Kulla Diflomasiyya: Akwai Kyakkawar Huldar Abota Tsakanin Sin Da Najeriya
[ad_1]
A yau ne ake cika shekaru 55 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen Sin da Najeriya. A wani bikin murnar ranar ta musamman da ya gudana a birnin Abuja a kwanakin baya, Joseph Tegbe, darekta-janar na kwamitin huldar abota da ta shafi manyan tsare-tsare ta Najeriya da Sin (NCSP), ya ce, hadin gwiwar da kasashen 2 suke yi ya zarce matsayin harkar diflomasiyya, tare da samar da dimbin sakamako masu amfanar da jama’a a zaman rayuwarsu na yau da kullum.
Cikin jawabinsa, Mista Tegbe ya ambaci wani sabon aikin kiwon kaji da aka kaddamar da shi a Najeriya a kwanan baya, wanda bangaren Sin ya samar da tallafi a ciki. Ana sa ran zuba dalar Amurka biliyan 1 wajen gudanar da aikin, inda za a yi kiwon kaji da yawansu ya kai fiye da miliyan 7, ta yadda za a rika samun kwai kimanin miliyan 6 a kowace rana, don samar da karin abinci ga mutanen Najeriya. Ban da haka, Mista Tegbe ya ambaci niyyar bangarorin Sin da Najeriya ta hadin gwiwa don sake gina masana’antar samar da karafa ta Ajaokuta, wadda a cewarsa za ta tabbatar da farfadowar masana’antar, da daidaita tsarin raya tattalin arzikin Najeriya, gami da mai da kasar ta zama cibiyar sarrafa kayayyaki ta nahiyar Afirka.
Haka zalika, a nasa bangare, wani mai nazarin al’amura masu alaka da kasashe masu tasowa na Najeriya mai suna Lawal Sale, ya rubuta wani bayani da ya shafi huldar dake tsakanin Najeriya da Sin, wanda aka wallafa a shafin kafar yada labaru ta “Economic Confidential”, inda ya bayyana huldar a matsayin mai samar da takamaiman sakamako. A cewarsa, bisa tsare-tsaren hadin gwiwa na “Ziri Daya Da Hanya Daya” da Dandalin Hadin Gwiwar Kasar Sin Da Kasashen Afirka, kasar Najeriya ta ci gajiyar dimbin ayyukan gina kayayyakin more rayuwar jama’a. A cikinsu har da layin dogo na Abuja-Kaduna, da na Lagos-Ibadan, da layin jirgin kasa na birnin Lagos, da na birnin Abuja, da tashar jiragen ruwa ta Lekki, da tagwan hanya ta Abuja-Keffi-Makurdi, da manyan gine-ginen zamani guda 6 da aka gina cikin wasu filayen tashi da saukar jiragen sama dake Najeriya, da dai sauransu.
Shin me ya sa huldar dake tsakanin Sin da Najeriya ke iya samar da dimbin sakamako masu inganci kamar haka? Dalili shi ne, bisa matsayinsu na bai-daya na kasashe masu tasowa, Sin da Najeriya suna da burin iri daya, wato zamanantar da al’umma da kyautata zaman rayuwar jama’a. Saboda haka, ba sa yarda da manufar kasashen yammacin duniya ta mai da kansu “masu jagorantar duniya” da neman ta da rikici bisa bambancin tunanin siyasa. Saboda haka, a yayin da wata babbar kasa dake yammacin duniya ta dauki matakan da suka hada da kara harajin kwastam, da hana shigowar mutane cikin harabarta, da kakaba laifin “keta hakkin dan Adam”, da barazanar kai hari, kan Nijeriya, a nasu bangare, kasar Sin da ta Najeriya suna kallon juna a matsayin abokan hulda na daidai-wa-daida, inda suke samar da sakamako a-kai-a-kai, ta hanyar hadin gwiwa a fannonin gina kayayyakin more rayuwa, da ilimi, da kiwon lafiya, da aikin gona, da dai sauransu.
Zuwa yanzu, Najeriya ta zame wa kasar Sin babbar abokiyar hulda ta farko a fannin aikin gini, kuma kasa ta biyu a fannin karbar kayayyakin da kasar Sin ta kera da fitarwa zuwa ketare, da zama abokiyar ciniki ta uku, da wurin da ake zuba wa jari mai muhimmanci a nahiyar Afirka. Ya zuwa watan Nuwamban shekarar 2025, jimillar darajar cinikin da aka yi tsakanin Sin da Najeriya ta zarce dalar Amurka biliyan 22 da miliyan 300, wadda ta nuna yanayi na samun karuwa cikin matukar sauri.
A wannan lokacin da ake murnar cika shekaru 55 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Najeriya, muna iya ganin yadda kasashen 2 ke ci gaba da zama ginshikai wajen samar da karuwa da hadin kai da kuma ci gaba a nahiyar Afirka, da tsarin hadin kan kasashe masu tasowa, da ma tsari na kasa da kasa.
Duk da cewa duniyarmu na cike da yanayin rashin tabbas, amma hadin gwiwar Sin da Najeriya yana ci gaba da samar da sakamako mai gamsarwa. Hakan ya shaida muhimmancin huldar abota ta daidai-wa-daida, da mutunta juna, da kokarin samar da sakamako mai inganci. (Bello Wang)
[ad_2]
Source link