Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa Ƙungiyar Da Ke Safarar Makamai Tare Da Kama Mutane 3 A Filato
[ad_1]
Dakarun Soji da haɗin guiwar JTF OPEP sun tarwatsa wata ƙungiya da ake zargin tana safarar makamai a yankin Vom da ke Jos ta Kudu a Jihar Filato.
An gudanar da aikin da safiyar ranar 24 ga watan Disamba, 2025, inda aka kama mutane uku da kuma ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu da aka ƙera a gida, harsasai, wuƙaƙe, da wayoyin hannu.
- Dangote Kaɗai Ba Zai Iya Wadatar Da Nijeriya Man Fetur Ba, In Ji Manyan ‘Yan Kasuwa
- Dangote Kaɗai Ba Zai Iya Wadatar Da Nijeriya Man Fetur Ba, In Ji Manyan ‘Yan Kasuwa
Yayin aikin, wasu matasa da mata sun kai wa sojoji hari, wanda hakan ya raunata ɗaya daga cikin jami’an, tare da lalata motar aikinsu, amma sojoji sun shawo kan lamarin.
Ana tsare waɗanda aka kama da makaman da aka ƙwato domin gudunar da bincike.
JTF ta yi kira ga ‘yan ƙasa da su yi aiki tare da jami’an tsaro, inda kuma ta yi gargaɗin cewa aikin doka babban laifi ne, tare da jaddada cewa za ta ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Jihar Filato.
[ad_2]
Source link