An cafke ’yan Najeriya 48 kan aikata damfara a Ghana

[ad_1]



’Yan Sandan a Ƙasar Ghana, sun kama ’yan Najeriya 48 a birnin Accra bisa zargin aikata damfara a intanet.

An kama su ne bayan wani samame da jami’an tsaro suka kai cikin dare.

Ministan Yaɗa Labaran Ghana, Sam George, ya ce dukkanin waɗanda aka kama ’yan Najeriya ne, maza 46 da mata biyu.

Ya bayyana cewa suna shiga ƙasar ne domin aikata laifukan damfara ta intanet.

A cewarsa, daga cikin laifukan da ake zarginsu da aikatawa akwai soyayyar ƙarya ta intanet, inda suke yaudarar mutane su tura musu kuɗi.

Hakazalika, ya ce akwai damfarar kasuwanci da neman masu zuba jari da kuma sayar da kaya na ƙarya.

Jami’an tsaron Ghana sun ce sun ƙwato kayan da suke amfani da su wajen aikata damfarar, ciki har da kwamfuta guda 54, wayoyi 39, da na’urar sadarwa ta Starlink.

Hukumomin Ghana suna gudanar da bincike a kansu, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu nan ba da jimawa ba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *